Na gamsu da hukuncin INEC na dage zabe - Wani minista ya yi caccaki 'yan adawa

Na gamsu da hukuncin INEC na dage zabe - Wani minista ya yi caccaki 'yan adawa

- Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya ce matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka na dage babban zaben kasar ya yi dai-dai

- Mr Shittu, ya ce wannan ba shi ne karon farko da INEC ta ke dage zabe ba a kasar ba, tare da cewa babu wani dalili na kashin kai ko wata manufa a dage zaben ba

- Sai dai mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Oyo, Musah Abdulwasi, ya bayyana wannan matakin na INEC a matsayin abun takaici

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya ce matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka na dage babban zaben kasar ya yi dai-dai, a cewarsa, hakan ne zai baiwa hukumar cikakken lokacin da za ta kammala shirye shiryenta kafin zuwan sabuwar ranar zaben da ta sanya.

Ministan ya bayyana hakan a ranar Asabar a garin Saki, jihar Oyo, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa hukumar INEC ta dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya daga ranar Asabar 16 ga watan Fabreru zuwa ranar 23 ga watan na Fabreru. Ya yin da zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki zai kasance a ranar 9 ga watan Maris.

KARANTA WANNAN: Zamantakewar aure: Ali Nuhu ya bada labarin yadda ya hadu da matarsa har ya aureta

Na gamsu da hukuncin INEC na dage zabe - Wani minista ya yi caccaki 'yan adawa

Na gamsu da hukuncin INEC na dage zabe - Wani minista ya yi caccaki 'yan adawa
Source: UGC

Mr Shittu, wanda ya ce wannan ba shi ne karon farko da hukumar zabe ta ke dage babban zabe ba a kasar ba, ya yi ikirarin cewa babu wani dalili na kashin kai ko wata manufa a dage zaben ba.

Ya kara da cewa lokacin da INEC ta bayar zai taimakawa jam'iyyarsa ta APC wajen karfafa yakin zabenta na dukkanin 'yan takara da ke takara a jam'iyyar.

Ministan ya kuma shawarci 'yan Nigeria da su guji 'yan siyasar da za su sayi kuri'unsu.

Sai dai mataimakin kakakin majalisar dokoki ta jihar Oyo, Musah Abdulwasi, ya bayyana wannan matakin na INEC a matsayin abun takaici.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel