Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna

Shugaba Muhammadu Buhari yana kan hanyarsa ta zuwa filin sauka da tashin jirage na Musa Yar'adua da ke Katsina domin dawowa babban birnin tarayya Abuja bayan hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dage zaben zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasar ya baro gidansa da ke GRA a Daura jihar Katsina misalin karfe 11 na safiyar yau bayan mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar da sanarwar shugaban kasar a kan dage zaben da INEC tayi.

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kasar ya isa Daura ne a jiya Alhamis domin ya kada kuri'ansa a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya amma daga bisani aka dage zaben.

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna
Source: UGC

Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna

Da duminsa: Shugaba Buhari ya baro Daura domin dawowa Abuja, hotuna
Source: Twitter

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Na Kasa (INEC) ta dage babban zaben 2019 kalubalen da ta fuskanta a wurin rabon kayayakin zabe zuwa wuraren da za ayi amfani da su.

Sanarwar dagewar ta fito ne daga bakin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu misalin karfe 2.45 na safiyar Asabar 16 ga watan Fabrairu bayan ya kammala taron gaggawa da hukumomin tsaro da masu sanya ido a kan zabe da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce ba zai yiwa a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara da farko ba hakan ya tilasta aka dage zaben da mako daya.

A yanzu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu yayin da zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi kuma za ayi a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel