Da duminsa: Rikici ya rutsa da hadimin gwamnan jihar Delta, an harbe shi har lahira

Da duminsa: Rikici ya rutsa da hadimin gwamnan jihar Delta, an harbe shi har lahira

Rahotannin da Legit.ng ta samu yanzu na nuni da cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun harbe mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Delta kan harkokin ci gaban matasa, Lawrence Ngozi Akpomiemie, inda ya mutu nan take.

Gidan talabijin na TVC ya ruwaito cewa an kashe Mr Akpomiemie a yayin da wani rikici ya barke a garin Ekpan, karamar hukumar Uvwie da ke jihar Delta a daren ranar Asabar.

Kafin mutuwarsa, Akpomiemie ya kasance mai tallafawa gwamna Okowa akan harkokin bunkasa rayuwar matasa.

KARANTA WANNAN: Dage zaben 2019: Atiku ya kwancewa Buhari, APC da INEC zani a kasuwa, ya ja hankalin 'yan Nigeria

Da duminsa: Rikici ya rutsa da hadimin gwamnan jihar Delta, an harbe shi har lahira

Da duminsa: Rikici ya rutsa da hadimin gwamnan jihar Delta, an harbe shi har lahira
Source: Depositphotos

Sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labarin, ba a san dalilin da ya haddasa rikicin da ya zama silar mutuwar hadimin gwamnan ba.

Duk wani yunkuri na tuntubar mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar Delta, DSP Andrew Aniamaka domin jin ta bakin rundunar ya ci tura.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel