PDP ta yi tur da dage zaben shugaban kasa, ta zargi APC da sa hannu a matakin INEC

PDP ta yi tur da dage zaben shugaban kasa, ta zargi APC da sa hannu a matakin INEC

- Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da hukuncin da INEC ta dauka na dage babban zaben kasar na 2019, daga ranar 16 ga watan Fabreru zuwa 23 ga watan Fabreru

- Shima Alhaji Atiku Abubakar ya yi tur da dage zaben kasar tare da zargin gwamnatin Buhari na zama silar faruwar wannan lamari

- Haka zalika, PDP ta ce INEC da APC sun dade suna kulla makirci domin dage zaben ta hanyar kona ofisoshin hukumar da lalata kayayyakin zabe a wasu jihohi

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, a ranar Asabar ya yi Allah wadai da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka na dage babban zaben kasar na 2019, daga ranar 16 ga watan Fabreru zuwa 23 ga watan Fabreru.

A cikin wata sanarwa daga mai magana a madadinsa, Ike Ibonyi, Mr Secondus ya bayyana wannan hukunci a matsayin makircin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da darewa akan karagar mulkin kasar duk da cewa ta bayyana karara 'yan Nigeria sun gaji da irin salon mulkinsa.

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da misalin karfe 2:40 na safiyar ranar Asabar, ya sanar da cewa hukumar ta dage zaben shugabar kasar, bayan da 'yan Nigeria suka kammala duk wani shiri na jefa kuri'unsu a ranar zaben.

KARANTA WANNAN: APC ta yi tur da dage zabe, ta ce akwai jita-jitar INEC na goyon bayan PDP

PDP ta yi tur da dage zaben shugaban kasa, ta zargi APC da sa hannu a matakin INEC

PDP ta yi tur da dage zaben shugaban kasa, ta zargi APC da sa hannu a matakin INEC
Source: Depositphotos

A yanzu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a ranar 23 ga watan Fabreru, yanyin da hukumar ta sanya ranar 9 ga watan Maris a matsayin ranar da za a gudanar sa zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki.

Yan Najeriya na ci gaba da yin Allah wadai da wannan mataki da hukumar INEC ta dauka a kurarren lokaci, inda da yawa ke sukar INEC akan gaza gudanar da zaben duk da cewa ta shafe shekaru kusan hudu tana ma zaben shiri.

Shima dan takarar shugabankasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi tur da dage zaben kasar tare da zargin gwamnatin Buhari na zama silar faruwar wannan lamari.

Mr Secondus ya yi zargin cewa APC tare da hadin bakin INEC sun dade suna kokarin ganin zaben bai gudana akan lokaci ba ta hanyar kona ofisoshin hukumar INEC a wasu jihohi da kuma lalata kayayyakin zabe, da nufin haddasa wata matsala da za ta zamar masu hujjar dage zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel