APC ta yi tur da dage zabe, ta ce akwai jita-jitar INEC na goyon bayan PDP

APC ta yi tur da dage zabe, ta ce akwai jita-jitar INEC na goyon bayan PDP

- Ofishin yakin neman zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi "Tur" da hukuncin da hukumar INEC ta dauka, na dage babban zaben kasar na 2019

- Haka zalika, INEC ta dage ranar zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki zuwa ranar 9 ga watan Maris, maimakon ranar 2 ga watan na Maris

- Sai dai a cikin wata sanarwa, ofishin yakin neman zaben shugaban kasar na APC, ya zargi INEC da hada baki da jam'iyyar PDP domin magudin zabe

Labarin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu, na nuni da cewa, ofishin yakin neman zaben tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi "Tur" da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka, na dage babban zaben kasar na 2019.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun tarayya daga ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, har sai ranar 23 ga watan na Fabreru.

Haka zalika, INEC ta dage ranar zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki zuwa ranar 9 ga watan Maris, maimakon ranar 2 ga watan na Maris.

KARANTA WANNAN: Ta tabbata: An daga zaben shugaban kasa

APC ta yi tur da dage zabe, ta ce akwai jita-jitar INEC na goyon bayan PDP

APC ta yi tur da dage zabe, ta ce akwai jita-jitar INEC na goyon bayan PDP
Source: Depositphotos

Sai dai sanarwar da Mr Festus Keyamo, mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben shugaban Najeriya ya fitar ta zargi INEC da hada baki da jam'iyyar hamayya ta PDP domin magudin zabe.

Ya ce: "Muna fatan INEC za ta kasance mai nuna rashin goyon bayan kowanne bangare a yayin gudanar da harkokin zabe, domin munanjin jita-jitar cewa wannan matakin hadin baki ne tsakanin INEC da jam'iyyar hamayya ta PDP, wacce da ma bata shiryawa zaben ba."

Masu sharhi dai na ganin dage zaben zai janyo wa hukumar zaben bakin jini da kuma sanya shakku a zukatan 'yan Najeriya game da shirnta na gudanar da sahihin zabe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel