Ta tabbata: An daga zaben shugaban kasa

Ta tabbata: An daga zaben shugaban kasa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Na Kasa (INEC) ta dage babban zaben 2019 kalubalen da ta fuskanta a wurin rabon kayayakin zabe zuwa wuraren da za ayi amfani da su.

Sanarwar dagewar ta fito ne daga bakin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu misalin karfe 2.45 na safiyar Asabar 16 ga watan Fabrairu bayan ya kammala taron gaggawa da hukumomin tsaro da masu sanya ido a kan zabe da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce ba zai yiwa a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara da farko ba hakan ya tilasta aka dage zaben da mako daya.

A yanzu, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu yayin da zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi kuma za ayi a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Ga sakon da hukumar ta INEC ta fitar a shafin ta na Twitter a kasa.

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

A cewar wasu rahotani, an kira taron gaggawar ne saboda kalubalen da hukumar ta fuskanta yayin rabon kayayakin zabe a wasu jihohi. An ruwaito cewa har misalin karfe 9 na daren jiya ana rabon kayayakin zabe a wasu jihohi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel