Tashin hankali: Yadda rayuka 66 suka salwanta cikin kwanaki 2 a wata jihar Arewa

Tashin hankali: Yadda rayuka 66 suka salwanta cikin kwanaki 2 a wata jihar Arewa

Mun kara samun muhimman bayanai akan yadda akayi wasu hatsabibai suka yiwa wasu kyauyuka kawanya tare da yiwa akalla mutane 66 kisan gilla tare da raunata wasu da dama a cikin satin da ya gabata a jihar Kaduna.

A cewar wani wanda lamarin ya auku akan idon sa, ya bayyanawa majiyar mu cewa harin guda biyu ne na farko a kan wasu 'yan kabilar Adara sannan kuma na biyun shine na ramuwar gayyayya akan wasu fulani da aka zarga da kai harin na fari.

Tashin hankali: Yadda rayuka 66 suka salwanta cikin kwanaki 2 a wata jihar Arewa

Tashin hankali: Yadda rayuka 66 suka salwanta cikin kwanaki 2 a wata jihar Arewa
Source: UGC

KU KARANTA: Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan dage zaben 2019

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar harin cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan. A cikin sanarwar, gwamnan ya yi tir da harin da aka kai kuma ya gargadi al'ummar akan daukan doka a hanunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel