Da duminsa: INEC ta kammala taron gaggawa, ta cimma matsaya a kan zabe

Da duminsa: INEC ta kammala taron gaggawa, ta cimma matsaya a kan zabe

Kakakin hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, Rotimi Oyekanmi ya ce hukumar ta kammala taron gaggawar da ta fara a daren Juma'a kuma ya ce hukumar ta cimma matsaya a kan zaben da Shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

The Cable ta ruwaito cewa Oyekanmi ya yi wannan jawabin ne a bayan taron gaggawar da INEC tayi a hedkwatan ta da ke babban birnin tarayya Abuja

Da duminsa: INEC ta kammala taron gaggawa, ta kuma cimma matsaya

Da duminsa: INEC ta kammala taron gaggawa, ta kuma cimma matsaya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna

Oyekanmi ya shaidawa menema labarai cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu zai yi musu jawabi a kan matsayar da hukumar ta cimma nan da kankanin lokaci.

Hukumar zaben ta kira taron gaggawa ne da masu ruwa da tsaki a harkar zabe domin tattaunawa a kan kalubalen da ke gabansu na rabon kayayakin zabe da yadda zai iya shafar gudanar da zaben.

Wasu na hasashen cewa mai yiwuwa INEC ta dage zaben zuwa wani lokaci nan gaba sai dai kawo yanzu hukumar bata tabbatar da hakan ba.

Ku biyo mu domin karin bayani...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel