Zaben 2019: Yan takara 23,213 zasu kara a zaben bana, kalli jerinsu

Zaben 2019: Yan takara 23,213 zasu kara a zaben bana, kalli jerinsu

Yayinda yan Najeriya ke shirin kada kuri'insu fari daga ranan Asabar, 16 ga watan Febrairu da ranan 2 ga watan Maris, Legit.ng ta kawo muku lissafin yawan yan siyasan da suke takara a zabubbuka daban-daban da za'a gudanar.

1' Jam'iyyun siyasa

Jam'iyyun siyasa tis'in da daya (91) sukayi rijista kuma zasu musharaka a zaben 2019

2. Yan takaran shugaban kasa

Yan takaran shugaban kasa saba'in da uku (73) da mataimakansu zasu kara a zaben da za'a gudanar ranan Asabar, 16 ga watan Febrairu.

3. Yan takaran gwamna

Yan takaran kujeran gwamna 1,063 da mataimakansu zasu kara a ranan 2 ga watan Maris, 2019.

4. Yan takaran majaisar dattawa

Yan takaran kujeran majalisar dattawa 1,904 ke takaran kujeru 109 a majalisar dattawan Najeriya.

5. Yan takaran majalisar wakilai

Yan takaran kujeran majalisar wakilai 4,680 ke takaran kujeru 360 a majalisar wakilan Najeriya.

6. Yan takaran majalisar jihohin jiha

Yan siyasa 14,643 ke neman kujeran yan majalisun dokokin jihohi daban-daban a fadin tarayya

7. Shugabannin kananan hukumomi a Abuja

Mutane 105 ke fafutukan kujerar shugabannin kananan hukumomi shida a birnin tarayya Abuja

8. Kansilolin birnin tarayya

Yan takara 701 ke neman kujerun kansiloli a birnin tarayya Abuja

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel