Ina nan a Najeriya ban je ko’ina ba, kuma zan fita jefa kuri’a gobe – Obasanjo

Ina nan a Najeriya ban je ko’ina ba, kuma zan fita jefa kuri’a gobe – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yana nan a ciki kasar Najeriya, babu inda ya je.

Hakan martini ne ga wasu rahotanni da ke yawo a kafafen sadarwa cewa tsohon shugaban kasar ya bar Najeriya sannan cewa ba zai samu damar halartan zabnen da za a gudanar a gobe Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

Obasanjo ya musanta wannan labara ne a yau Juma’a, 15 ga watan Fabrairu a babban dakin karatun shi mai suna (OOPL) da ke garin Abeokuta.

Ina nan a Najeriya ban je ko’ina ba, kuma zan fita jefa kuri’a gobe – Obasanjo

Ina nan a Najeriya ban je ko’ina ba, kuma zan fita jefa kuri’a gobe – Obasanjo
Source: UGC

Ya kuma bayyana cewa yana daga cikin mutanen da suka taimaka wajen kafa damokradiyya a kasar nan, don haka bai ga dalilin da zai sa ya fice daga kasar nan ba a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gabatar da manyan zabukka ba.

KU KARANTA KUMA: Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku

Obasanjo ya kara da cewa; Ina da matukar jure ma irin wannan sharrin da ake min, a cikin al’ummar mu ta Yarbawa ana gane darajar mutum da yadda yake mu’amala da masu yada sharri, duk mai son yada karya ko sharri akan ka ya yi ta yi, amma dai wani abu da muka yi imani da shi shine, akwai ranar kin dillanci, Allah zai yi maganin masu aikata sharri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel