Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan dage zaben 2019

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan dage zaben 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tsokaci a kan dage babban zaben shekarar 2019 da hukumar zabe mai zaman kanta INEC tayi a safiyar yau bisa dalilan rashin isar kayayakin zabe wuraren da ya dace.

A sakon da fadar shugaban kasar ta fitar, shugaba kasar ya bayyana rashin jin dadinsa game da dage zabe duba da irin tabbacin kasancewa cikin shiri da hukumar zaben ta rika bawa 'yan Najeriya da kasashen waje sai gashi kwatsam ta dage zabe cikin sa'o'i kadan kafin fara zaben.

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan dage zaben 2019

Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan dage zaben 2019
Source: Facebook

Sakon ta cigaba da cewa, "yan Najeriya da dama sun bar garuruwan da suke zaune zuwa inda za suyi zabe kuma masu sanya idanu a kan zabe na kasashen waje duk sun iso Najeriya.

"Ita kanta INEC ta bawa kasar tabbacin cewa ta kammala shiri domin gudanar da zaben a lokuta da dama kuma hakan ya sa dukkan 'yan kasa sunyi imanin cewa za ta gudanar da zaben kamar yadda ta tsara da farko.

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

"Gwamnati na bawa INEC dukkan kudaden da ta ke bukata domin shirya zaben kana ta kame daga yin katsalandan cikin ayyukan hukumar zaben.

"Muna kira ga INEC ta tabbatar da cewa dukkan kayayakin zabe sun isa inda ya dace kuma kada a bari su shiga hannun bata gari. Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da 'yan Najeriya su bawa INEC hadin kai domin ganin demokradiyar mu ta dore.

"Ina kira ga dukkan 'yan Najeriya su kasance masu biyaya da doka kuma su guji tayar da zaune tsaye domin tabbatar da cewa demokradiyar mu ta cigaba.

"A halin yanzu zan kama hanya domin komawa Abuja domin tabbatar da cewa an samu nasarar gudanar da taron da INEC ta kira na masu ruwa da tsaki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel