Zaben shugaban kasa: Jihohi 10 da za'a fafata tsakanin Buhari da Atiku

Zaben shugaban kasa: Jihohi 10 da za'a fafata tsakanin Buhari da Atiku

Gabanin zaben da zai gudana gobe Asabar, 16 ga watan Febrairu, 2019. Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu bayanai game da yadda zaben shugaban kasa musamman tsakanin manyan abokan hamayya biyu na jam'iyyar All Progressives APC da Peoples Democratic Party PDP.

Akwai wasu jihohi Najeriya goma mafi yawan jama'a da sukayi rijistan zabe tsakanin shekarar 2015 da 2018. Manyan abokan hamayya a zaben na, shugaba Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zasu kara wadannan jihohi.

1. Jihar Legas

Bisa ga lissafin hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC, Mutane 6,570,291 sukayi rijistan zabe za jihar. Jihar Legas dai yankin kabilan Yarbawa ne amma akwai kabilu daban-daban da suka zamar da Legas tamkar mahaifarsu.

2. Jihar Kano

Bisa sanarwan INEC, Mutane 5,457,747 ne sukayi rijistan zaben a Kanon Dabo, kasancewan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam'iyyar adawa ta PDP, za'a fafata tsakanin manyan yan takaran a gobe

3. Jihar Kaduna

INEC ta bayyana cewa mutane 3,932,492 ne sukayi rijistan zabe a jihar Kaduna. alkaluma sun bayyana cewa akwai mabanbanta ra'ayi da dama a jihar kasancewar yawan kabilu da sabanin addini da ya jihar Kaduna ta shahara dashi. Saboda haka, sai dai an ga sakamako

4. Jihar Katsina

Lissafin INEC ya bayyana cewa mutane 3,100,000 suka karbi katin zabensu a jihar Katsina wacce take mahaifar daya daga cikin dan takaran kujeran. Yayinda wasu ke ganin cewa ko shakka babu shugaba Buhari zai lashe, wasu sunce sai dai an tashi saboda yan siyasar hamayya irinsu tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shema da Lado Danmarke.

5. Jihar Rivers

Da kadan jihar Katsina tafi jihar RIvers yawan mutanen da sukayi rijista kuma za'a fafata tsakanin shugaban kamfen Buhari, Rotimi Ameaechi da gwamnan jihar, Nyesom Wike.

6. Jihar Oyo

Mutane 2,934,107 ne sukayi rijista a jihar. Duk da jihar jam'iyyar APC ne, masu sharhi na ganin cewa za'a raba kuri'un ne

7. Jihar Delta

Bisa ga rahoton INEC, mutane 2,845,274 ne sukayi rijista a jihar Delta. Sai an tashi, amma jihar PDP ce

8. Jihar Plateau

Kimanin mutane miliyan biyu da rabi sukayi rijista a jihar Plateau hakazalika jihar Benue

9. Jihar Benue

10. Jihar Bauchi

Bisa ga rahoton INEC, mutane 2,462,843 ne sukayi rijista a jihar Bauchin Yakubu.

Allah yasa an wanye lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel