Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja

Ko sama ko kasa: An nemi kuri'un kananan hukumomi 2 an rasa a Neja

A yau, Juma'a ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a jihar Neja ta ce akwai yiwuwar ba za a gudanar da zabukkan sanata a mazabun Neja ta Arewa da Neja ta Kudu ba a ranar Asabar saboda kuri'un zabe da aka tanadar domin mazabun sun bace.

Bataren zabe na jihar, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a garin Minna.

Da duminsa: An nemi wasu kuri'un zabe a jihar Neja an rasa

Da duminsa: An nemi wasu kuri'un zabe a jihar Neja an rasa
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

"Mun sanar da hedkwatan INEC da ke Abuja domin a dauki mataki cikin gaggawa.

"Jami'an babban bankin kasa CBN da aka daurawa nauyin kulawa da kayayakin zabe masu muhimmanci sun tafi Abuja domin karba kayayakin zabe da za ayi amfani da su a goba Asabar saboda haka muna jira muji abinda zai kasance," inji shi.

Egwu ya ce an samar da kashi 85 cikin 100 na kayayakin zabe da ake bukata a jihar kuma tuni an rarrabar da wasu kayayakin zaben zuwa kananan hukumomi 25 da ke jihar kawai abinda ya rage sune kayayakin masu muhimmanci.

Ya ce hukumar ta horas da ma'aikatan wucin gadi guda 23,000 da za suyi aikin zabe a jihar.

Baturen zaben ya kuma ce mutane 2,181,400 ne za su kada kuri'arsu a babban zaben na kasa a jihar Neja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel