Da duminsa: An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna

Da duminsa: An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna

A kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.

Da duminsa: An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna

Da duminsa: An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da afkuwar harin cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan. A cikin sanarwar, gwamnan ya yi tir da harin da aka kai kuma ya gargadi al'ummar akan daukan doka a hanunsu.

Gwamnatin ta ce ta tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma an fara kama wadansu da ake zarginsu da hannu a cikin harin.

"Gwamnatin jihar ta mika ta'aziyarta ga iyalan wadanda suka mutu. An kuma tura jami'an tsaro zuwa garin har ma an kama wasu da ake zargi da hannu a harin," a cewar gwamnatin jihar.

"Ana gudanar da bincike a kan harin kuma babu shakka za a binciko wadanda suka aikata harin a hukunta su.

"Muna kira da mazauna garin Kaduna su kasance masu zama lafiya domin samun gudanar da zabe a cikin lumana da kwanciyar hankali," inji gwamnati

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel