Kasa da sa’o’i 24 dattawan APC sun bar jam’iyyar zuwa PDP a jihar Plateau

Kasa da sa’o’i 24 dattawan APC sun bar jam’iyyar zuwa PDP a jihar Plateau

Kasa da sa’o’i 24 zuwa zaben 2019 na kasa wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Gyel dake a kudancin jihar Filato sun sauya sheka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) don marawa Alhaji Atiku Abubakar baya, a zaben shugaban kasa.

Daya daga cikin mambobin kungiyan yakin neman zaben Gwamna Lalong, Hon. Pam Tizah, wanda aka fi sani da Ashasha ne ya jagoranci sauya shekar kusan mutane dari daga jam’iyyar APC a ranar Juma’a a lokacin wani taro na jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa jam’iyyar bata da manufa.

Hon. Tizah, wanda ya kasance tsohon shugaban PDP a karamar hukumar kudancin Jos ya bar jam’iyyar PDP a 2017 tare da shugaban kwamitin majalisar wakila, Hon. Edward Pwajok (SAN) sannan ya sauya sheka daga jam’iyyar APC don haduwa da Pwajok wanda tsohon shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya karbi bakuncinsa a jam’iyyar PDP.

Kasa da sa’o’i 24 dattawan APC sun bar jam’iyyar zuwa PDP a wata jihar Plateau

Kasa da sa’o’i 24 dattawan APC sun bar jam’iyyar zuwa PDP a wata jihar Plateau
Source: Depositphotos

Ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP zata lashe zaben shugaban kasa da na yan majalisa a ranar Asabar daga sama har kasa don yanta yan Najeriya daga wahalar yunwa da rashin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Filato, Hon. Dalyop Jonathan Bok, wanda ya bar jam’iyyan a 2017 ya bayyana komawarsa jam’iyyar a matsayin dawowa gida.

Shugaban kungiyan dattawan jam’iyyar PDP a yankin Gyel, Gyang Mali Jok ya bayyana farin cikinsa cewa masu sauya sheka zasu karawa jam’iyyar PDP muhimmanci a lokacin zabe da za a gudanar a ranan Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel