Muhimman ababe da ya kamata ku sani game da zaben 2019

Muhimman ababe da ya kamata ku sani game da zaben 2019

A gobe Asabar, 16 ga watan Fabrairu, al'ummar Najeriya za su yi tururuwa wajen jefa kuri'un su domin zaben kujerar shugaban kasa da kuma kujeru na 'yan majalisar tarayya da za su jagorance su tsawon shekaru hudu masu gabatowa.

Muhimman ababe da ya kamata ku sani game da zaben 2019

Muhimman ababe da ya kamata ku sani game da zaben 2019
Source: UGC

Kazalika a ranar Asabar, 2, ga watan Maris na shekarar da muke ciki, za a gudanar da zaben kujerun gwamnoni da kuma na 'yan majalisun dokoki na jihohin kasar nan

A yayin da za a gudanar da babban zabe, tsawon kimanin shekaru 20 kenan da kasar Najeriya ta koma kan tsari da kuma tafarki na Dimokuradiyya yayin da dakarun soji na mulkin mallaka suka mika akalar jagorancin ta a hannun farar hula a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999.

Ga jerin wasu muhimman ababe da ya kamata ku sani game da babban zaben kasa na bana

1. Kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta bayyana, a halin yanzu akwai adadin masu rajistar zaben bana 84,004,084, inda a zaben 2015 da ya gabata aka samu masu rajistar zabe kimanin 67,422,005.

2. Akwai rufunan zabe 119,973 da za a al'ummar kasar nan za su kada kuri'un su a bana.

3. Yayin da yankin Arewa maso Yamma ke sahun farko na adadin masu rajistar zabe kimanin 20,158,100, yankin Kudu maso Yamma da ya kunshi jihar Legas, Ekiti, Ondo, Ogun, Osun, da kuma Oyo ya biyo baya da adadin masu rajista 16,292,212.

4. Yankin Kudu maso Gabas ne mafi kankanta ta fuskar adadin masu rajistar zabe kimanin 10,057,130. Arewa maso Gabas na da masu rajistar zabe 11,289, 293. Yayin da Kudu maso Kudu ke da masu rajista 12,841,279, yankin Arewa ta Tsakiya na da adadin masu rajista kimanin 13,366,070.

5. Jihar Legas na kan gaba da fuskar yawan adadi na masu rajistar zabe kimanin 6,048,156, inda jihar Kano ke bi ma ta baya da kimanin masu rajistar zaben 5,149,070.

6. Jihar Bayelsa ce ta karshen baya mai adadin masu rajistar zabe 754,394, yayin da garin Abuja ke bi ma ta baya da kimanin 952, 815

7. Jam'iyyu 91 ne za su fafata a tsakanin su yayin babban zabe na 2019.

8. Akwai 'yan takara 1,904 da ke hankoron kujeru 109 na majalisar dattawa, yayin da 'yan takara 4,680 ke fafutikar samun nasarar maye gurbin kujeru 360 na majalisar wakilai.

9. INEC ta tanadi ma'aikata 814,453 da za su gudanar da harkokin zabe cikin garin Abuja da kuma dukkanin jihohi 36 da ke fadin kasar nan.

10. Hukumar INEC ta tantance kungiyoyi 116 na nan cikin gida da za su sanya idanun lura kan babban zabe yayin da ta bayar da damar sanya idanu yayin zaben ga kungiyoyi 28 na kasashen ketare.

11. 'Yan takara 72 ke fafutikar lashe zaben kujerar shugaban kasa da a za a gudanar a gobe Asabar, 16, Fabrairu.

12. Akwai 'yan takarar gwamna 2,412 da za su fafata cikin jihohin kasar nan a ranar 2 ga watan Maris.

13. Majalisar dattawan Najeriya ta bayar da sahalewar ta akan batar da N189,207,544,893 domin gudanar da harkokin zabe na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel