Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku

Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku

Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar yace babu ma’aikacin gwamnati da ba a taba yiwa zargin rashawa ba.

Yayinda yake jawabi a hira tare CNN, Atiku yace zarge-zarge da ake yi akan shi duk kage ne bai aikata ba.

“Babu ma’aikacin gwamnati da ba ayiwa zargin rashawa,” a cewar Atiku. Atiku, wanda aka yiwa zargin rashawa sau da dama na cigaba da karyata duk wani laifi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi hasashen cewa nasararsa ne dalili da yasa ake alakanta sunan shi da rashawa, ya kalubalanci duk mai ganin yana da shaida da yazo ya gabatar akansa, sannan a gurfanar da shi domin fuskantar hukunci.

Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku

Babu wani jami’in gwamnati da ba a zarga da rashawa ba - Atiku
Source: Facebook

“Na cimma nasarori, ba a taba gurfanar dani ba, ba a taba kai karana ba, duk zarge-zarge ne. Na bukaci kowa, na kalubalanci mutane a bainar jama’a, cewa idan akwai wani mai shaida a kaina, ya fito ya gabatar,” a wata hira da yayi da CNN.

A lokacin da aka yi mishi tambayan ko yana da hannu a rashawa, Atiku yace: “a’a, saboda idan na kasance da hannu cikin rashawa, da anyi karana kuma da an gurfanar dani”.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso ya yi godiya ga mutanen Kano kan yadda suka yi tururuwar fitowa kamfen din PDP

Yayinda aka yi masa tambayan akan nuna daidaito tsakanin jinsi, Atiku yace a kidan jam’iyyar PDP, jinsi abune muhimmi, kuma zata nada mata a matsayin shuwagabannin, mambobin majalisa, da ministoci a gwamnatinta.

Ya sha alashin cewa zai sake duba ga lamarin aikin soji dake a matakai na kasa, wadanda suka sadaukar da rayukansu don samar da kwanciyar hankali ga yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel