Na kashin baya: Jerin jam’iyyu 18 da basu da dan takarar shugaban kasa a zaben 2019

Na kashin baya: Jerin jam’iyyu 18 da basu da dan takarar shugaban kasa a zaben 2019

A yayin da ake saura kwana daya a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, duk da hayaniyar da ta dabaibaye farfajitar siyasar Najeriya ashe akwai wasu jam’iyyu da basu tsayar da dan takarar shugaban kasa ba, asali ma basu da wani gwani.

Idan za’a tuna a yanzu haka akwai jam’iyyu 91 dake da rajista da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, daga cikin akwai guda saba’in da uku, 73, da suka tsayar da yan takara, yayin da guda goma sha takwas basu da dan takarar shugabancin kasar Najeriya.

KU KARANTA: Bincike ya tabbatar akwai isashshen sinadarin iskar gas a Gombe da Bauchi – shugaban NNPC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadannan jam’iyyu goma sha takwas sun hada da:

Congress of Patriots (COP)

Alternative Party of Nigeria (APN)

Legacy Party of Nigeria (LPN)

Modern Democratic Party (MDP)

Movement for The Restoration and Defence of Democracy (MRDD)

New Generation Party (NGP)

New Progressives Movement (NPM)

Alliance for Democracy (AD)

Peoples Democratic Movement (PDM)

Peoples Progressives Party (PPP)

Socialist Party of Nigeria (SPN)

United Peoples Congress (UPC)

United Progressives Party UPP)

Young Democratic Party (YDP)

Youth Party (YP)

Zenith Labour Party (ZLP)

Democratic Alternative (DA)

Sai dai ko a cikin jam’iyyu 73 dake da yan takarar shugaban kasa, akwai wasu guda biyu da suka gamu da matsalolin cikin gida, daga cikinsu akwai jam’iyyar ACPN da kuma jam’iyyar SDP, inda yar takarar shugabancin kasa a ACPN ta janye takararta, amma INEC ta ce bata isa ba, don haka akwai hoton jam’iyyarsu a takardar zabe.

Yayin da aka samu rikici wajen tabbatar da wanene sahihin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP, inda ake jayayya tsakanin tsohon minista Jerry Gana da tsohon gwamnan jahar kros ribas Donald Duke, wanda har ta kai ga uwar jam’iyyar ta sallamesu duka daga jam’iyyar, sa’annan ta bayyana Buhari a matsayin dan takararta, amma duk da haka an riga an buga takardar zabe da hoton jam’iyyar.

Sai dai wasu jam’iyyun da basu fitar da dan takarar shugaban kasa ba sin bayyana matsalar karancin kudaden gudanar da takarar a matsayin abinda ya janyo musu tsaiko, kamar yadda shugaban jam’iyyar MRDD, Alhaji Danjuma Ali ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel