Ana kasa da sa'o'i 24 zabe, APC ta samu karuwa akalla 100,000 da PDP, SDP a Sokoto

Ana kasa da sa'o'i 24 zabe, APC ta samu karuwa akalla 100,000 da PDP, SDP a Sokoto

Malam Bashir Mani, mai magana da yawun jagoran APC a jihar Sokoto, Sanata Aliyu wammako, yace maigidansa ya karbi bakuncin sabbin masu sauya sheka daga jam'iyyar PDP da SDP ranan Laraba daga yakin Sokoto ta Arewa da kudu.

Sama da mutane 88,000 wadanda suka kunshi shugabannin jam'iyyar Social Demcratic Party SDP daga kananan hukumomin jihar 23 na jihar suka dawo jam'iyyar APC.

Sauran sune shugabannin da mambobin babban jam'iyyar gwamnan jihar, Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Goronyo suka dawo tafiyar Wamakko.

Wasu mambobin kungiyar yan kasuwar Kanawa ne a karamar hukumar Sokoto ta kudu, yayinda sauran yan Kofar Atiku, kwaryan Sokoto ne da sauransu.

Sanata Aliyu Wamakko ya tarbi wadannan masu sauya shekan cikin karamci musamman a wannan lokaci.

KU KARANTA: Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Yace: "Muhawarar yan takaran gwamna da aka gudanar a jihar Sokoto ta fiddamu kunya, dan takaranmu, Alhaji Ahmed Aliyu, matashi ne wanda ya cancanta ya jagoranci jihar da kuma kara mata girma."

"Kana muhawarar ta kara tona asirin babban aboki hamayyarsa cewa baida alkibla kan ayyukan da za'ayiwa jama'ar jihar ba."

"Barin in kara jaddada cewa idan aka zabesa, dan takaranmu da abokin tafiyarsa zasu share cutan da akeyi da sunan kudin makaranta, yayinda za'a biya ma'aikata dasu."

Wamakko ya kara kira ga jama'ar jihar su zabi shugaba Muhammadu Buhari da yan takaran APC a dukkan kujeru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel