Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)

Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)

Wani bidiyo ya billo inda Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bukaci mutanen jihar Kwara da sub a shugaban kasa Muhammadu Buhari kaso 90% na kuri’unsu.

NAN ya ruwaito cewa an nadi bidiyon ne a Ilorin a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu, ranar karshe na gangamin yakin neman zabe.

Saraki ya kasance darakta-janar na kamfen din dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar.

Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)

Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)
Source: Depositphotos

Bisa ga dukkanin alamu tiuntuben harshe Saraki ya samu a wajen gangamin domin wata murya ta gyara masa furucin nasa inda tace ‘Atiku’.

Shugaban majalisar dattawar na gwagwarmayar ganin ya dawo kan kujerarsa na majalisar dattawa inda yake karawa da abokin adawarsa na jam’iyyar All Progressives Congress Ibrahim Oloriegbe. Oloriegbe ya sha alwashin fatattakar Saraki zuwa gida.

Kuna iya kallon bidiyon anan.

KU KARANTA KUMA: Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

A halin da ake ciki, mun ji cewa Kasa da sa’o’i 24 zuwa zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabrairu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya samu babban garkuwa yayinda jam’iyyar Alliance for Democratic (AD) mara masa baya.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa hukuncin goyon bayan Atiku ya biyo bayan ganawar da jam’iyyar tayi a Abuja inda ta saki jawabanta ga manema labarai a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta tattaro cewa sanarwar goyon bayan PDP na dauke da sa hannun shugaban kungiyar na yankin kudu maso yamma, Otunba Tayo Onayemi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel