Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

Dan majalisa mai wakiltar al’ummar mazabar Kog ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Mista Ahmed Ogembe ya gamu da mummunan hatsari a ranar Juma’a, 15 ga watan Feburairu, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan ya gamu da hatsarin ne akan hanyar Abuja zuwa Lokoja, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garinsu Okene, domin shirye shiryen gudanar da zaben gobe, inda za’a zabi shugaban kasa, Sanatoci da yan majalisun dokoki.

KU KARANTA: Tsagerun IPOB sun kona ofishin Yansanda, sun lakada ma yansanda dan banzan duka

Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

Motar
Source: UGC

A yanzu haka Mista Ogembe yana neman tazarce a kujerarsa ta Sanatan Kogi ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zabukan da za’a gudanar a gobe Asabar, 16 ga watan Feburairu.

Hadimin Sanatan ta bangaren watsa labaru, Duke Opeyemi ne ya tabbatar da hatsain maigidan nasa, inda yace lamarin ya faru ne da misalin kargfe 9 na safiyar Juma’a a daidai kauyen Gegu dake cikin karamar hukumar Kotonkarfe.

Wani Sanata daga cikin Sanatocin Najeriya ya tsallake rijiya da baya a hadarin mota

Motar
Source: UGC

Kaakakin Sanatan, Mista Duke Opeyemi ya bayyana cewa motar Sanatan wanda aka kerata don kada harsashi ya bulata ta yi ta wuntsulawa sau ba iyaka har sai da ta tsaya da kanta, amma cikin ikon Allah daga Sanatan har abokan tafiyar tashi basu samu wani rauni ba.

Shima Sanatan ya bayyana wannan lamari a matsayin jarrabi daga Allah, inda ya bayyana godiyarsa ga Allah daya kareshi, sa’annan yayi addu’ar Allah ya cigaba da kareshi, da iyalansa da kuma kafatanin al’ummar mazabansa gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel