Bayan iftila'in gobara: INEC ta buga sabon kundin masu zabe, ta bude sabon ofishi a Filato

Bayan iftila'in gobara: INEC ta buga sabon kundin masu zabe, ta bude sabon ofishi a Filato

- Hukumar INEC ta ce ta kammala sake buga dukkanin kundin masu rejista na kowacce rumfar zabe a karamar hukumar Qua'an da ke jihar Filato

- Haka zalika INEC ta ce ta bude wani sabon ofishinta da ke karamar hukumar, bayan da gobara ta lalata wancan

- A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa gobara ta tashi a ofishin INEC na karamar hukumar Qua'an, inda ta kone duk wasu muhimman kayayyaki da ke a ciki

Wata mota makare da akwatunan zabe kundin masu zabe ta isa karamar hukumar Qu'an, jihar Filato, domin musanya kayan zaben da gobara ta kona su kurmus a kwanakin baya. A cewar wata sanarwa daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta kammala sake buga dukkanin kundin masu rejista na kowacce rumfar zabe.

Haka zalika INEC ta ce ta bude wani sabon ofishinta da ke karamar hukumar, bayan da gobara ta lalata wancan.

Idan za a iya tunawa, a baya bayan nan gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC na karamar hukumar Qua'an da ke jihar Filato, inda ta kone duk wasu muhimman kayayyaki da ke a ciki.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Amurka ta yiwa Atiku Abubakar babban albishir kan zaben ranar Asabar

Bayan iftila'in gobara: INEC ta buga sabon kundin masu zabe, ta bude sabon ofishi a Filato

Bayan iftila'in gobara: INEC ta buga sabon kundin masu zabe, ta bude sabon ofishi a Filato
Source: Depositphotos

Jami'in hulda da jama'a da ilimantar da masu kad'a kuri'a na hukumar INEC, Osaretim Imaehorobo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadin makon da ya gabata.

"Wani mai gadi ne da ya yi shaye-shaye ya haddasa gobarar," a cewar sanarwar.

Gobarar ta lalata wasu katunan zabe na din-din-din da jama'a basu kaiga karba ba, da dai sauran kayayyaki da suka hada da kundin masu zabe, akwatunan zabe da sauransu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel