Tsaro lokacin zabe: Yansanda 12,500 aka turo Kaduna jiya zuwa yau

Tsaro lokacin zabe: Yansanda 12,500 aka turo Kaduna jiya zuwa yau

- Hukumar yan sandan jihar Kaduna tace ta watsa yan sanda sama da 12,500 don tsaro a zaben asabar

- Hukumar tace babu yan sintiri cikin jami'an tsaron amma akwai sauran cibiyoyin tsaro da zasu tallafa

- Kwamishinan yan sandan jihar yayi kira ga yan siyasa da kada su saka yan bangar siyasa a lamarin

Zabe: Bai kamata a bari APC

Zabe: Bai kamata a bari APC
Source: UGC

Hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar juma'a tace ta tura sama da jami'an tsaro 12,500 a sassan jihar don zaben ranar asabar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar DSP Yakubu ya sanar da ofishin dillancin labarai a Kaduna.

Sabo yace jami'an tsaro da suka hada da Immigration, Custom da jami'an NSCDC zasu samar da cikakken tsaro domin tabbatar da anyi zabe cikin zaman lafiya.

Yace hukumar ta yi binciken guraren barazanar tsaro saboda a kara jami'ai don tabbatar da masu zabe da sauran yan kasa an tsare lafiyar su.

Mai magana da yawun hukumar ya jaddada cewa za a samar da matakan tsari don hana duk wani shiri na masu hargitsa gurin zaben.

Akan jita jitan baza yan sintirin cikin gari, Sabo yace babu wannan tsarin.

GA WANNAN: Ka tona manyan barayin da suke wurinka neman mafaka in kai mai gaskiya ne - gwamnan PDP ga Baba

Yace kwamishinan yan sanda, Ahmad Abdur-Rahman ya bayyana cewa baza a saka masu tsaron gargajiya ba don tsaron zabe.

"Yan sanda kadai da sauran jami'an tsaro da sukayi na zaben jiha su zasu yi wannan ma, bazamu bar yan sintiri su samar mana da tsaro yayin zabe ba," inji Sabo.

Ya roki masu zabe dasu tallafawa jami'an tsaro da sauran cibiyoyin da bayanai masu amfani da zasu tabbatar da anyi zaben a cikin kwanciyar hankali.

"Wannan kiran nayi shi ne ga yan siyasa; kada kuyi amfani da yan bangar siyasa don daukewa masu zabe da sauran yan kasa hankali. Zasu samar da bayanai masu amfani don a kawo musu tallafin gaggawa."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitterr https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel