INEC: Dama can basu shirya ba, sun jaza wa jama'a asarar lokaci da kudi - Balarabe Musa

INEC: Dama can basu shirya ba, sun jaza wa jama'a asarar lokaci da kudi - Balarabe Musa

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa yace hukumar zabe ta kunyata shi amma bai yi mamaki ba

- Tsohon gwamnan yace dama can hukumar bata shiryawa zaben ba sakamakon kalubalen da take fuskanta

- Ya hori yan Najeriya dasu kwantar da hankalin su yayin jiran sabuwar ranar zaben

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, a ranar asabar yace INEC sun kunyata shi sakamakon daga zaben da tayi, amma yace hukumar zabe bata shirya ma zaben ba tun farko.

INEC ta sanar da dage zaben ne a sa'o'i kadan saura a fara zaben shugaban kasa na 16 ga watan Fabrairu da zaben majalisar wakilai wanda Shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmood Yakubu yake jagoranta.

Yayin bada sanarwar dage zaben, shugaban hukumar a Abuja yace "kalubalen da suka fuskanta na aiyuka ne" suka sa aka dage zaben.

Hukumar ta maida 23 ga watan fabrairu da 9 ga watan maris a matsayin sabbin ranakun zaben shugaban kasa da majalisar dattawa da na gwamnoni da majalisar jiha.

Amma a tattaunawa da ofishin dillancin labarai da Musa yayi a jihar Kaduna a ranar asabar, yace ya kunyata amma abin bai bashi mamaki ba.

GA WANNAN: Yadda Boko Haram suka kai mana hari a jiya - Gwamna Shettima

"Banyi mamaki ba saboda dama INEC bata shirya zaben ba, gani da matakin shirye shiryen su. INEC na da babbar matsala ta fannin kudi, abinda majalisar dattawa ta ba wa hukumar ba zai isheta ba kuma kowa ya san hakan,"

"Bamu ma san ko nawa ne kudin da gwamnatin tarayya ta bawa hukumar ba."

Akwai manyan kalubalen tsaro da zasu iya kawo cikas ga hukumar a yayin zaben.

"Jami'an tsaro na fuskantar kalubalen kudi kuma suna cike da tsoro."

Kalubalen da ma'aikatar shari'a kuwa ke fuskanta ya taka babban rawa wajen dage zaben, inji Musa.

"Don haka dole ince sun kunyata ni amma banyi mamaki ba. Ina fatan duk masu ruwa da tsaki na hukumar zasu dau matakin kawo karshen kalubalen da hukumar ke fuskanta kafin ranar 23 ga watan Fabrairu saboda sai anyi zabe ne shugaban kasa zai iya mika mulki."

Musa yayi kira ga yan Najeriya dasu kwantar da hankalin su yayin jiran ranar zaben

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel