Akwai jihohin da har yanzu lamurra basu dawo daidai ba bayan n rufe ko'ina don zabe

Akwai jihohin da har yanzu lamurra basu dawo daidai ba bayan n rufe ko'ina don zabe

- Har yanzu dai Dutse, babban birnin jihar Jigawa bai wartsake ba

- Bayan an dage zaben amma har yanzu garin bai koma yanda yake ba

- Tituna masu cinkoso shiru, ta kuma shagunan siye da siyarwa garkame

Akwai jihohin da har yanzu lamurra basu dawo daidai ba bayan n rufe ko'ina don zabe

Akwai jihohin da har yanzu lamurra basu dawo daidai ba bayan n rufe ko'ina don zabe
Source: Twitter

Titunan Dutse har yanzu kamar an share su babu hada hadar mutane, wato babban birnin jihar Jigawa.

Duk da dage zaben da hukumar zabe mai zaman kanta tayi, har a safiyar asabar shiru kake ji a titunan babban birnin na Jigawa. Babu hada hadar jama'a balle kai da komowar su.

Cunkoson ababen hawa a titin Hakimi da yafi ko ina cinkoso a babban birnin jihar ta Jigawa yau babu. Sai dai akan samu daidaikun ababen hawa dake yawo akan titin.

GA WANNAN: Yadda Boko Haram suka kai mana hari a jiya - Gwamna Shettima

Shaguna da sauran guraren kasuwanci akan titin Takur Adua duk a kulle amma kuma kadan daga cikin mazaunan yankin zaka hanga sun hada yan kungiyoyi ko gungu suna tattaunawa akan cigaban.

Daya daga cikin masu achaba, Usman Dan'auta, yace da yawan su ba mazauna babban birnin jihar bane, suna rayuwa ne a kananan kauyukan dake da makwaftaka da babban birnin jihar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel