Banbance-banbance 5 tsakanin zaben 2015 da kuma na 2019

Banbance-banbance 5 tsakanin zaben 2015 da kuma na 2019

Yayin da ya rage saura 'yan awanni kadan 'yan Najeriya su soma kada kuri'ar su a zaben gama gari da zai gudana a dukkan fadin kasar na shugaban kasa da kuma 'yan majalisar tarayya da suka hada da Sanatoci da kuma wakilai, mun shirya maku makala domin anfanin ku.

A cikin wannan makalar dai mun yi kokarin tattaro maku wasu muhimman banbance-banbance akalla guda 5 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta bullo da su tun bayan zabukan shekarar 2015.

Banbance-banbance 5 tsakanin zaben 2015 da kuma na 2019

Banbance-banbance 5 tsakanin zaben 2015 da kuma na 2019
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An kama buhunnan dangwalallun kuri'u 7 a jihar Jigawa

1. A zaben 2019 hukumar INEC ta yi tanadin yadda makafi za su kada kuri'a ta hanyar samar da takardarsu ta zabe ta daban da kuma abin da suka saba rubutu da shi da ake kira 'braile' a turance.

Ga masu lalurar makanta da ba su yi karatu ba, hukumar INEC ta ce za su iya zuwa da jagora daga gida a wajen zabe.

An kuma yi tanadin wani babban gilashi a rumfar zabe ga zabaya masu lalurar gani, wadanda idan rana ta yi sosai ba su iya gani ba.

2. Sabanin yadda aka yi a 2015 inda sai an tantance ka sannan daga baya ka dawo ka kada kuri'a, a zaben 2019 mutum zai iya jefa kuri'arsa nan take bayan an tantance shi.

Mai jefa kuri'a da zarar ya zo an tantance shi da na'urar card reader, sai a ba shi kuri'arsa kai tsaye ya shiga ya kada wa jam'iyyar da yake so ba tare da ya yi jinkiri ba.

3. An kara fadada rumfar zabe zuwa rassa domin saukake wa masu zabe, inda za a iya tantance mutum uku a lokaci daya cikin sauki maimakon cunkushewa a rumfa daya.

Amma INEC ta ce ba wai an kara rumfa ba ne ko an canza rumfa ba.

4. Ko wace rumfar zabe tana da jami'an zabe guda hudu, kuma ko wane jami'i aikinsa daban, wadanda za a gansu sanye da wasu tufafin da ke tabbatar da jami'an zabe ne.

5. INEC tace yin amfani da card reader a zabe wajibi ne domin an yi amfani da ita kuma an ga amfaninta.

Hukumar ta ce an kara inganta na'urar fiye da wadanda aka yi amfani da su a zaben 2015.

Kuma wadanda za a yi amfani da su sun fi aiki cikin hanzari fiye da na 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel