Da duminsa: Amurka ta yiwa Atiku Abubakar babban albishir kan zaben ranar Asabar

Da duminsa: Amurka ta yiwa Atiku Abubakar babban albishir kan zaben ranar Asabar

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samu yanzu yanzu, na nuni da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta zanta da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar kan babban zaben kasar da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru.

Sakataren harkokin kasashen waje na kasar Amurka, Mr Mike Pompeo, ya kira Atiku Abubakar a wayar salula a safiyar ranar Juma'a, inda ya bashi tabbacin cewa kasar Amurka za ta duk mai yiyuwa na ganin cewa an gudanar da sahihin zabe a Nigeria.

KARANTA WANNAN: Hukumar INEC: Muna kan nazarin bukatar Malami ta dage zaben jihar Zamfara

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku, ya ce ya samu kiran waya daga sakataren harkokin kasashen wajen Amurka, Mr Pompeo, inda suka tattauna muhimman abubuwan da suka shafi zaben kasar, tare da samun tabbaci na cewa kasashen waje za su sa ido don ganin an gudanar da sahihin zaben da babu magudi a ciki.

Da duminsa: Amurka ta yiwa Atiku Abubakar babban albishir kan zaben ranar Asabar

Da duminsa: Amurka ta yiwa Atiku Abubakar babban albishir kan zaben ranar Asabar
Source: Facebook

Atiku ya ce: "A safiyar yau na samu kiran waya daga skaataren harkokin kasashen waje na Amurka, Mr Mike Pompeo, wanda ya bani tabbacin cewa kasashen waje musamman Amurka za sun dukufa don ganin an gudanar da sahihin zabe a Nigeria."

Atiku ya kuma yiwa al'ummar kasar fatan alkairi a lokacin da za su gudanar da zabukansu a fadin kasar, tare da yin addu'ar Allah ya albarkaci kasar Nigeria da al'ummar da ke rayuwa a cikinta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel