PDP ta tanadi daloli domin saye bakin masu ruwa da tsaki a zabe - APC

PDP ta tanadi daloli domin saye bakin masu ruwa da tsaki a zabe - APC

- Jam'iyyar APC tayi ikirarin cewa jam'iyyar PDP ta tanadi makuden kudi da za ta raba wa jihohi domin saye bakin hukumomin da ke da hannu cikin zabe

- A cewar jam'iyyar ta APC, PDP za tayi hakan ne domin tana fargaban za ta sha kaye a babban zaben gobe Asabar

- Jam'iyyar ta APC ta ce ayi amfani da kudaden ne domin saye bakin jami'an INEC, hukumomin tsaro da masu sa ido a zabe

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana zargin babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da bawa masu ruwa da tsaki a harkar zabe cin hanci domin su ba su fifiko.

A cikin sanarwar da kakakin jam'iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu ya fitar ya ce jam'iyyar adawan tana aikata hakan ne saboda tana tsoron shan kaye a zaben.

Zabe: APC tana zargin PDP da bawa masu ruwa da tsaki cin hanci

Zabe: APC tana zargin PDP da bawa masu ruwa da tsaki cin hanci
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: An kama buhu 14 makare da kuri'u da aka dangwale

"Jam'iyyar adawa ta fara bawa hukumomi da masu ruwa da tsaki a zabe cin hanci na kudi da niyyar samun goyon bayansu gabanin zaben da ke tafe."

Premium Times ta ruwaito cewa jam'iyyar ta APC ta ce tuni babban jam'iyyar adawar ta kammala shirin yada za ta raba kudade ga wasu muhimman mutane da hukumomi da ake ganin suna da rawar da su taka a zaben.

Sai dai jam'iyyar ta APC ba ta bayar da hujja a kan wannan zargin da tayi ba.

Ta yi ikirarin cewa jam'iyyar PDP ta kammala shirin rabar da kudu tsakanin dallan Amurka miliyan biyar zuwa 10 ga jihohin Najeriya domin 'zirga-zirga da tara al'umma' a ranar zaben.

A cewar jam'iyyar na APC, wadanda PDP za ta bawa cin hancin sun hada da jami'an INEC, hukumomin tsaro da masu sanya idanu a kan zabe saboda su kawar da kai a yayin da jam'iyyar ke tafka magudin zabe.

APC kuma tayi ikirarin cewa PDP na amfani da wasu marubuta da ba a san ko su wanene ba domin a kafafen sada zumunta domin suka ga hukumomin da ke da ruwa da tsaki a zabe.

Hakan yasa jam'iyyar tayi kira ga dukkan mutane suyi taka tsan-tsan da irin wadannan mutanen da makircin da jam'iyyar adawar ke kulla wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel