Hukumar INEC: Muna kan nazarin bukatar Malami ta dage zaben jihar Zamfara

Hukumar INEC: Muna kan nazarin bukatar Malami ta dage zaben jihar Zamfara

- INEC ta ce ta karbi wata wasika daga hannun babban Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'a, inda ya bukaci hukumar da ta dage zaben jihar Zamfara

- Malami ya aikewa hukumar INEC da wasika, tare da wasu muhimman takardu, inda ya ta'allaka bukatarsa da hukuncin da wata kotu ta yi kan rikicin siyasar na jihar

- Sai dai, INEC ta ce har yanzu ta na ci gaba da nazarin wasikar, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za ta sanar da matsayarta kan wannan bukata

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta karbi wata wasika daga hannun Abubakar Malami, babban Antoni Janar na kasa kuma ministan shari'a, inda ya bukaci hukumar da ta dage zaben jihar Zamfara.

Malami ya aikewa hukumar INEC da wasika, tare da wasu muhimman takardu, inda ya ta'allaka bukatarsa da hukuncin da wata kotu ta yi na umurtar hukumar da ta amincewa jam'iyyar APC gabatar da 'yan takara a zabe mai zuwa.

Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin ilimantar da masu kad'a kuri'a da watsa labarai, ya tabbatar da cewa hukumar ta karbi wannan wasika tare da muhimman takardun.

KARANTA WANNAN: An bankado 'yan majalisun tarayya na APC guda 4 da ke amfani da takardun bogi a Bauchi

Hukumar INEC: Muna kan nazarin bukatar Malami ta dage zaben jihar Zamfara

Hukumar INEC: Muna kan nazarin bukatar Malami ta dage zaben jihar Zamfara
Source: UGC

Sai dai, ya ce hukumar har yanzu na ci gaba da nazarin wasikar, yana mai cewa nan ba da jimawa ba za ta sanar da matsayarta kan wannan bukata.

"Hukumar ta karbi wannan wasika da Antoni Janar na kasa ya aiko. Hukumar na nazarin wannan wasikar da kuma sauran takardun da ke tare da ita. Hukumar za ta sanar da matsayarta nan ba da jimawa ba." a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel