Yanzu-yanzu; Walter Onnoghen ya musanta zargin da ake masa, kotu ta bashi beli

Yanzu-yanzu; Walter Onnoghen ya musanta zargin da ake masa, kotu ta bashi beli

Gurfana ta kankama da safiyar Juma'a misalin karfe 10:30 a kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT inda sallamammen alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya bayyana.

Shugaban kotu CCT, Danladi Umar, ya tsaya kan bakansa cewa Walter Onnoghen bai isa ya zauna cikin mamun jama'a ba sai dai cikin kwandon mai laifi. Ba tare da gaddama, Jastis Walter Onnoghen, ya shiga ciki amma yaki zama.

Ya ce ba zai zauna kan kujerar da aka basa ba kuma ya gwammace ya tsaya a tsaye.

Bayan hakan sai Jastis Danladi Umar ya bada umurnin a karantawa Walter Onnoghen laifukan da ake zarginsa da su. Ya musanta dukkan laifukan.

Daga karshe, kotun CCT ta basa beli bisa ga sanayya. An daga karar zuwa ranan 11 ga watan Maris, 2019.

Ku saurari cikakken rahoton....

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel