Masu ritaya 243,166 sun karbi N7.82bn a matsayin fansho cikin watan Janairu kacal

Masu ritaya 243,166 sun karbi N7.82bn a matsayin fansho cikin watan Janairu kacal

Hukumar Fansho ta bayyana cewa ta biya masu ritaya 243,166 kimanin naira biliyan 7.82 a matsayin kudin fansho a watan Janairu 2019.

A wani rahoto kan ayyukan hukumar PTAD a watan Janairu, 2019 ta nuna cewa ta biya masu karban fansho 101,702 kimanin Biliyan 1.71 sannan ta biya wasu rukunin yan fansho kimanin naira biliyan 4.94 a watan.

Rahoton ya kuma nuna cewa yan sanda masu ritaya 15,892 sun samu naira miliyan 552.61 sannan hukumar Kula da shige da fice da kuma hukumar gidan yari sun samu naira miliyan 615.76 a wannan watan.

Masu ritaya 243,166 sun karbi N7.82bn a matsayin fansho cikin watan Janairu kacal

Masu ritaya 243,166 sun karbi N7.82bn a matsayin fansho cikin watan Janairu kacal
Source: UGC

A bangaren hukumar fansho na ma’aikatan gwamnatin an rahoto cewa sabbin yan fansho 133 aka tantance a watann Janairu, sannan 90 daga cikinsu yan fanshon ne na ainahi yayinda 41 suka kasance magada.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Kungiyar Kiristoci sun mara wa Atiku baya

Hukumar ta kuma bayyana cewa yan fansho sama da 2800 da basa cikin jerin sunayen wadanda za a biya an ware su domin a sake duba kan lamarinsu sannan an mayar da 11 cikin wadanda za a biya, yayinda aka dakatar da wasu 309 saboda asusun hadin gwiwa, an kuma cire mutane 103 saboda sun mutu.

Hukumar ta kuma magance korafe-korafem yan fansho da bashin da suke bi wanda gaba daya ya kama naira miliyan 2.65 da yan fansho takwas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel