Zaben 2019: Kungiyar Kiristoci sun mara wa Atiku baya

Zaben 2019: Kungiyar Kiristoci sun mara wa Atiku baya

- Kungiyar Kiristoci sun tsayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a matsayin dan takararsu

- Kungiyar ta kuma yi kira da Kiristoci da su zabi Atiku a matsayin shugaban kasa a zaben da za a gudanar a gobe Asabar

- COCGGDN ta zargi gwamnatin shugaba Buhari da rashin kokari da nuna wariya wajen nade-naden mukamai

Gabannin zaben ranar Asabar 16 ga watan Fabrairu, gamayyar kungiyar Kiristoci na Coalition of Christian Groups for Good Governance in Nigeria and Diaspora (COCGGDN) a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu sun tsayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a matsayin dan takararsu.

Kungiyar ta kuma yi kira da Kiristoci da su zabi Atiku a matsayin shugaban kasa a zaben da za a gudanar a gobe Asabar.

Zaben 2019: Kungiyar Kiristoci sun mara wa Atiku baya

Zaben 2019: Kungiyar Kiristoci sun mara wa Atiku baya
Source: UGC

Kungiyar tace ta yanke shawarar ne saboda ganin akwai bukatar hakan, inda tace ta lura da rashin kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar ta COCGGDN, Injiniya Daniel Kadzai yayinda yake karanto wasikat kungiyar a karshen wata ganawa da suka yi a Abuja, ya lissafa inda gwamnatin Buhari ta gaza wandca suka hada da son kai wajen nade-naden mukamai, yiwa kiristoci ritaya da wuri, kin cika alkawarin kawo karshen Boko Haram a shekaru hudu da kuma rashin magance kasha-kashen da makiyaya ke yi.

KU KARANTA KUMA: Duk wanda ya fallasa masu sayen kuri’a za mu biya shi lada – EFCC

Sakamakon wadannan abubuwa da kungiyar ta lissafa, tace ta yi watsi da sake neman takarar shugaba Buhari sannan ta zabi Atiku a matysayin dan takararta a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel