Asiri ya tonu: Yadda INEC ta sanya sunan matattu miliyan 1 a cikin rejistar masu zabe - PDP

Asiri ya tonu: Yadda INEC ta sanya sunan matattu miliyan 1 a cikin rejistar masu zabe - PDP

- Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa INEC ta sanya sunayen sama da matattu miliyan daya a rejistar masu zabe

- Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya ce sun gano cewa INEC ta yi hakan ne da zummar yin magudi domin baiwa Buhari da APC damar cin zabe

- PDP ta bukaci INEC da ta kasance mai bin doka da oda, tana mai cewa bai kyautu ace hukumar ta biyewa masu son a dage zaben jihar Zamfara ba

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya sunayen matattau 1,050,051 a cikin kundin rejistar masu kad'a kuri'a, da zummar yin magudi a babban zaben kasar, domin baiwa dan takarar jam'iyyar APC Muhammadu Buhari damar lashe zaben.

A cewar Secondus wanda ya zanta da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, an buga katin zaben din-din-din na matattun, wanda kuma aka raba su a fadin kasar.

Shugaban jam'iyyar APC ya roki hukumar INEC da ta kakkabe rejistar masu kad'a kuri'a kafin fara zaben. Ya kuma yi kira ga kwamitin zaman lafiya na kasa da ya zamo mai sa ido sosai domin tabbatar da ganin anyi sahihin zabe.

KARANTA WANNAN: Gani ga wane: Dan majalisa ya rasa mukaminsa bayan da ta bayyana ya saci burodi

Asiri ya tonu: Yadda INEC ta sanya sunan matattu miliyan 1 a cikin rejistar masu zabe - PDP

Asiri ya tonu: Yadda INEC ta sanya sunan matattu miliyan 1 a cikin rejistar masu zabe - PDP
Source: Twitter

Secondus wanda ya yi ikirarin cewa akwai tuggun da aka kitsa na yiwa 'yan kasashen waje rejistar zabe, musamman daga kasashen Niger da Kamaru, ya kara da cewa wannan ne ma dalilin da ya sa INEC ta bullo da rumfunan zaben a iyakokin kasar Nigeria da Kamaru da kuma Niger.

Ya yi kira ha hukumar INEC da ta kasance mai bin doka da oda a kowanne lokaci, yana mai cewa bai kyautu ace hukumar ta mayar da hankali kan masu cewa a dage zaben jihar Zamfara ba.

"Gazawar jam'iyyar APC na gabatar da 'yan takara a Zamfara sakamakon gaza gudanar da zabukan fitar da gwani kamar yadda dokar INEC ta tanadanar baya kunshe a cikin sashe na 28 da 39 na dokar zabe ta kasa 2010, ba kamar yadda shi AGF ke ikirari ba," a cewar Secondus.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel