Yanzu-yanzu: Uwar bari: Walter Onnoghen ya bayyana a kotun CCT

Yanzu-yanzu: Uwar bari: Walter Onnoghen ya bayyana a kotun CCT

Sallamammen shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Nkanu Onnoghen, ya isa zauren kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT.

Ya isa kotun misalin karfe 9:40 na safen nan tare motoci shida da suka rakosa yana sauraron zuwan alkalin kotun, danladi Umar.

A ranan Laraba, Kotun ladabta ma'aikatan gwamnati, CCT, ta baiwa sufetan yan sanda, IG Mohammed Adamu, umurnin damke sallamammen shugaban alkalai, Walter Nkanu Onnoghen, kuma ya gurfanar da shi gaban kotun ranan Juma'a.

Yayinda aka koma sauraran karan a kotu, gwamnatin tarayya ta bukaci Alkalin kotun CCT ta bada umurnin damke Walter Onnoghen tun da ya ki zuwa kotun cikin lumana.

Lauyan gwamnati, Aliyu Umar, ya mika bukatar ne a ranan Laraba, 13 ga watan Febrairu, 2019 inda ya nuna bacin ransa kan taurin kan Walter Onnoghen.

Amma alkalin kotun CCT, Jastis Danladi Umar, tare da wasu alakai biyu sunyi watsi da bukatar lauyan Onnoghen kuma suka baiwa jami'an tsaro umurnin kawo Onnoghen kotun ranan Juma'a.

Yace: "Ina son in ga abin zargi (Walter Onnoghen) cikin akwatin laifi ranan Juma'a"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel