Gani ga wane: Dan majalisa ya rasa mukaminsa bayan da ta bayyana ya saci burodi

Gani ga wane: Dan majalisa ya rasa mukaminsa bayan da ta bayyana ya saci burodi

- Sakamakon tonuwar asirinsa, kan satar burodi samfurin sandwich a wani shago da ke birnin Lublyana, wani dan majalisa ya yi murabus daga aikinsa

- Mr Krajcic wanda dan jam'iyya mai mulkin kasar ce ta Marjan Sarec List (LMS) ne, ya bayyana abin da ya faru a majalisar, inda ya labartawa abokan aikinsa komai

- Kafin zuwansa majalisa, Mista Krajcic ya taba zama malamin makaranta

Sakamakon tonuwar asirinsa, kan satar burodi samfurin sandwich a wani shago da ke birnin Lublyana, wani dan majalisa ya yi murabus daga aikinsa, bayan da ya bayyana cewa ya saci burodin ne saboda ma'aikatan shagon sun ki kula shi a lokacin da ya shiga siyayya shagon.

Kamar yadda dan majalisar, Mr Darij Krajcic na kasar Slovenia ya shaidawa manema labarai, "na fusata a lokacin da na je siyayya shagon amma ma'aikatan shagon suka nuna kamar ma babu wani mutum da ya zo siyayya, wannan ne ya sa na gwada tsarin tsaron shagon, ta hanyar fita da burodin ba tare da na biya kudi ba."

Duk da cewa Mista Krajcic ya nemi da a yi masa afuwa bayan da ya yi nadamar abun da ya aikata, sai dai ya bayyana cewa "bayan na saci burodin na fita da shi ba tare da na biya kudi ba, na dawo daga baya na biya su kudinsu."

KARANTA WANNAN: Mun kammala shiri kan zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun tarayya - INEC

Gani ga wane: Dan majalisa ya rasa mukaminsa bayan da ta bayyana ya saci burodi

Gani ga wane: Dan majalisa ya rasa mukaminsa bayan da ta bayyana ya saci burodi
Source: UGC

Mr Krajcic wanda dan jam'iyya mai mulkin kasar ce ta Marjan Sarec List (LMS) ne, ya bayyana abin da ya faru a majalisar, inda a wani taro na wani kwamiti da ya ke cikinsa, ya labartawa abokan aikinsa komai.

"Na tsaya a gaban kantar shagon na tsawon akalla minti uku," inji dan majalisar mai shekara 54 a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Channel POP.

Kafin zuwansa majalisa, Mista Krajcic ya taba zama malamin makaranta.

Da farko abokan aikinsa 'yan majalisa sun dauki abin da wasa, amma ranar Alhamis sai shugaban wani tsagi na jam'iyyar LMS Brane Golubovic ya soki abin da Mista Krajcic yayi.

An dai zabi Mista Krajcic ne a watan Satumbar bara, a lokacin da jam'iyyar Firai Minista Marjan Sarec ta LMS ta zama babbar kawa a hadakar jam'iyyu masu mulkin kasar Slovenia.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel