Zabe saura yan sa’o’i: APC ta yi babban kamu a jihar Oyo

Zabe saura yan sa’o’i: APC ta yi babban kamu a jihar Oyo

- Shugaban jam’iyyar ADP a jihar Oyo, Cif Folaranmi Owolabi, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar

- Owolabi ya sauya shekar ne tare da wasu mamobin jam'iyyar sama da 10,000

- Ya kuma sha alwashin hada kan sauran masu sauya shekar domin suyi kamfen wajen ganin nasarar yan takarar APC a zabe mai zuwa

Shugaban jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) a jihar Oyo, Cif Folaranmi Owolabi, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tare sa mamobin jam’iyyar sama da 10,000.

Da suke nuni akan zagewar tsohon gwamnan jihar da dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, Cif Adebayo Alao-Akala, masu sauya shekar sun bayyana cewa basu yi danasanin daukar wannan mataki ba kasa da sa’o’i 24 kafin zaben kasar.

Owolabi ya sha alwashin hada kan sauran masu sauya shekar domin suyi kamfen wajen ganin nasarar dan takarar kujerar sanata na yankin kudancin Oyo a APC, Gwamna Abiola Ajimobi; dan takarar gwamnan jihar, Cif Adebayo Adelabu da sauran mambobin APC.

Zabe saura yan sa’o’i: APC ta yi babban kamu a jihar Oyo

Zabe saura yan sa’o’i: APC ta yi babban kamu a jihar Oyo
Source: Depositphotos

Shugaban APC a jihar, Cif Akin Oke, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Mista Lekan Adeyemo ne ya tarbi masu tsoffin mambobin na ADP zuwa APC, a sakatariyar jam’iyyar da ke Oke-Ado, Ibadan.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigon PDP a birnin tarayya ya sauya sheka zuwa APC

Da yake jawabi ga masu sauya shekar, mataimakin Shugaban APC yace: “Ina matukar farin ciki da ganin cewa kun gane cewar a a wajen da ya dace kuke ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel