Wani babban jigon PDP a birnin tarayya ya sauya sheka zuwa APC

Wani babban jigon PDP a birnin tarayya ya sauya sheka zuwa APC

- Wani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Abubakar Sidi ya sauya sheka zuwa APC

- Alhaji Sidi wanda ya kasance tsohon jagoran kamfen na yakin neman zaben Goodluck/Sambo a 2015, yace ba zai iya ci gaba da kasancewa PDP saboda yanayin shugabannin jam’iyyar na yanzu

- Sidi yace lamarin tsaro a Najeriya ya inganta sosai sannan cewa an rage yawan talauci, rabuwar kabilanci, addini da kuma bangaranci sosai tun bayan da APC ta hau mulki a 2015

Wani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Abubakar Sidi, yace ya janye daga jam’iyyar sannan ya koma da akalaar siyasarsa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a babban birnin tarayya, Abuja.

Alhaji Sidi wanda ya kasance tsohon jagoran kamfen na yakin neman zaben Goodluck/Sambo a 2015, yace ba zai iya ci gaba da kasancewa PDP saboda yanayin shugabannin jam’iyyar na yanzu, wadanda suka yasar da kudirin wadanda iyaye wadanda suka asassa jam’iyyar.

Wani babban jigon PDP a birnin tarayya ya sauya sheka zuwa APC

Wani babban jigon PDP a birnin tarayya ya sauya sheka zuwa APC
Source: UGC

Yace ya matukar ji kunya kan abunda ya bayyana a matsayin tozarci da yaudara da sabbi shugabanni ke yi ta hanyar karkatar da jam’iyyar da kuma mayar da tsoffin mambobin jam’iyyar saniyar ware.

Sidi yace lamarin tsaro a Najeriya ya inganta sosai sannan cewa an rage yawan talauci, rabuwar kabilanci, addini da kuma bangaranci sosai tun bayan da APC ta hau mulki a 2015.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: PDP ta koka kan yawan matakan tsaron da aka tura Kwara

Yace gwamnati mai mulki na iya bakin kokari wajen ganin ta gyara barnar da akayi a baya don haka ta cancanci karin shekaru hudu domin cewa itace za ta lashe zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel