Mun kammala shiri kan zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun tarayya - INEC

Mun kammala shiri kan zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun tarayya - INEC

- INEC ta ce ta kammala duk wasu shirye-shirye na gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya a ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, 2019

- Babban bankin Nigeria shine ya samar da manyan motoci da za a dauki kayan daga filin jirgin sama na jihohi zuwa sauran garuruwa

- A cewar sa, tuni na'urorin tantance masu kad'a kuri'a da takardun dangwala zaben suka isa da yawan kananan hukumomi

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta kammala duk wasu shirye-shirye na gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya a ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru, 2019.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin ilimantar da masu kad'a kuri'a da watsa labarai, Festus Okoye, a shaidawa jaridar Daily Trust cewa tuni hukumar ta kammala duk wasu shirye-shirye na ganin cewa an samu gagarumar nasara a yayin gudanar da zaben har zuwa lokacin fadin sakamako.

"Muna daf da kammala raba kayayyakin gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisu a fadin kasar. Wasu daga cikin kayayyakin ana daukarsu daga Abuja zuwa Fatakwal zuwa Kano, yayin da jihohi mafi kusa na daukar kayansu daga Kano. Misali kayayyakin zabe na Kano da Jigawa, ana daukarsu ne daga filin jirgi na Kano. Babban bankin Nigeria shine ya samar da manyan motoci da za a dauki kayan daga filin jirgin sama na Kano zuwa sauran wurare."

KARANTA WANNAN: Tattaunawa: El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta gaza cafke Atiku

Mun kammala shiri kan zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun tarayya - INEC

Mun kammala shiri kan zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun tarayya - INEC
Source: Facebook

Mr Festus Okoye ya ce kayayyakin shiyyar Kudu maso Kudu kuwa an kaisu filin jirgi na Fatakwal. Inda ya bayyana cewa mafi akasarin kayan na da girma da nauyi, wanda ya sa manyan jiragen daukar kayane kadai za su kaisu wuraren da ake bukata.

"Kamar dai yau (jiya), rundunar sojin sama na amfani da jirginta na C-130 da kuma jirage kirar Hercules, domin dauka da rarraba kayan zaben. Muna fatan zasu kammala rarraba kayan gobe (yau) ta yadda za a samu damar rarrabawa kananan hukumomi," a cewar Okoye.

A cewar sa, tuni na'urorin tantance masu kad'a kuri'a da takardun dangwala zaben suka isa da yawan kananan hukumomi, kuma manyan jami'an gudanar da zaben sun daura damarar isa wuraren da aka tura su.

Okoye ya bayyana cewa jirgin da ke dauke da kayayyakin Maiduguri ya gaza sauka a garin kasancewar akwai hazo wanda ya tilasta shi komawa Abuja, "daga bisani muka tura kayan Kano, inda a yanzu su ke kan hanyar su ta zuwa Maiduguri."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel