Tattaunawa: El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta gaza cafke Atiku

Tattaunawa: El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta gaza cafke Atiku

- Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kasar Amurka ta gaza cafke Atiku Abubakar saboda kasancewarsa dan takarar shugaban kasa a Nigeria

- Gwamnan ya bayyana cewa Amurka ba za ta iya cafke Atiku ba ko da kuwa suna tuhumarsa, saboda cafke shi kamar tsoma hannu ne a sakamakon zaben kasar

- El-Rufai ya jaddada cewa, ba za a iya gane cewa ko Atiku na da ikon zuwa Amurka ko akasin hakan a yanzu ba, har sai bayan an kammala zaben 2019, idan ya sha kasa

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kasar Amurka ta gaza cafke dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda kasancewarsa dan takarar wata babbar jam'iyya, a cewarsa, cafke Atiku zai kawo tarnaki a sakamakon zaben kasar.

A zantawarsa da jaridar Premium Times, El-Rufai ya ce: "Ikon kowacce kasace ta baiwa mutum takardar izinin shiga kasar ko ta hana shi, ba na tunanin wannan wani sabon lamari ne. Duk yadda aka yi dai, ina da tabbacin cewa Amurka ba ta hana Atiku Visa ba. Ina da yakinin cewa suma suna son ya shiga kasar ta su, kawai dai shine bai gabatar da wannan bukatar ba tun tuni."

Gwamnan ya ce a lokacin da Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, to kusan a lokacin ya samu wata kariya na shiga kowacce kasa ya fito lafiya, "ko da suna tuhumarsa, dole ne su janye wannan tuhumar saboda cafke shi kamar tsoma hannu ne a sakamakon zaben kasar mai zuwa."

KARANTA WANNAN: Yanzunnan: Atiku ya samu goyon baya daga 'yan takarar shugaban kasa guda 2

Tattaunawa: El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta gaza cafke Atiku

Tattaunawa: El-Rufai ya bayyana dalilin da ya sa Amurka ta gaza cafke Atiku
Source: Depositphotos

El-Rufai ya jaddada cewa, ba za a iya gane cewa ko Atiku na da ikon zuwa Amurka ko akasin hakan a yanzu ba, har sai bayan an kammala zaben 2019, idan ya sha kasa, lokacin da babu kariya ta dan takarar shugaban kasa a kansa.

Wasu na zargin tsohon mataimakin shugaban kasar ne da kasa zuwa Amurka saboda zargin da aka ce kasar na yi masa na cin hanci da rashawa. Zargin da Atiku ya sha musantawa a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Janairu, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa kasar Amurka a yammacin ranar Alhamis.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, ya je kasar ne domin tattaunawa da jami'an kasar da kuma 'yan Najeriya mazauna kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel