Zaben 2019: Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar mata ta jam’iyyar APC

Zaben 2019: Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar mata ta jam’iyyar APC

Wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da shugabar mata ta jam’iyyar APC a jahar Delta, Uwargida Magaret, wanda yar gani kashenin Sanatan mazabar Delta ta tsakiya ne, Sanata Ovie Omo-Agege, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi garkuwa da Magaret ne a lokacin da take kan hanyarta ta dawowa daga wani gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar APC da aka yi a garin Orogun cikin karamar hukumar Ughelli ta Arewa, a ranar Talata.

KU KARANTA: Siyasa yar ra’ayi: Sarkin Daura ya bayyana ra’ayinsa game da takarar Buhari a zaben 2019

Zaben 2019: Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar mata ta jam’iyyar APC

Magaret
Source: UGC

Magaret na tare da wasu mutane uku ne a motar wani daga cikin daraktocin yakin neman zaben Sanata Omo Agege ne a lokacin da yan bindigan suka tare motarsu, sai dai sauran mutane ukun sun tsira da kyar.

Jim kadan bayan yin awon gaba da ita ne sai yan bindigan suka kira wani abokin Magaret, inda suka nemi a kai musu kudi naira miliyan Talatin (N30,000,000) kafin su saketa, abokin mai suna Kwamanda yace yan bindigan sun yi ta kiransa da barazanar kashe Magaret idan bai kai musu kudin ba.

Kwamanda ya bayyana ma majiyarmu cewa masu garkunwa sun bashi daman yin magana da Magaret na tsawon mintuna biyu domin ya tabbatar tana hannunsu kuma da ranta, zuwa yanzu dai yace yana ta basu hakuri akan su daga masa kafa don ganin yadda zai samo kudaden daga wajen yan uwanta.

“Duk kokarin neman yan uwanta da nayi ban samu nasara ba, amma shugaban jam’iyyar APC na mazabarmu ya bayyana min cewa Sanata Omo Agege na sane da lamarin, kuma Sanatan ma da kansa ya tabbatar min da cewa yana da labarin sace Magaret kuma yana iya kokarinsa don ganin an saketa.” Inji shi.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin rundunar Yansandan jahar Ribas game da lamarin yaci tura, sakamakon kaakakin rundunar, Andrew Aniamaka baya amsa wayar da aka yi masa, kuma bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel