Tsagerun IPOB sun kona ofishin Yansanda, sun lakada ma yansanda dan banzan duka

Tsagerun IPOB sun kona ofishin Yansanda, sun lakada ma yansanda dan banzan duka

Wasu gungun tsageru da ake zargi yayan kungiyar IPOB ne sun banka ma ofishin Yansandan Najeriya dake unguwar Ajali, cikin karamar hukumar Orumbo ta Arewa ta jahar Anambra, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Feburairu, inda tace a sa’ilin da tsagerun ko kokarin banka ma caji ofis din wuta sai da suka lakada ma jami’an Yansandan da suka tarar a ofishin dukan tsiya.

KU KARANTA: Siyasa yar ra’ayi: Sarkin Daura ya bayyana ra’ayinsa game da takarar Buhari a zaben 2019

Tsagerun IPOB sun kona ofishin Yansanda, sun lakada ma yansanda dan banzan duka

Ofishin Yansanda
Source: UGC

Bugu da kari bayan sun banka ma ofishin wuta, tsagerun sun kwance miyagun mutanen dake tsare a ofishin, sa’annan suna ta ihun ‘Babu zabe a kasar Biyafara’, wannan ne ya tabbatar da zargin da ake yin a cewa yayan kungiyar IPOB ne.

Idan za’a tuna, jagoran kungiyar IPOB dake rajin samar da kasar Biyafara, Nnamdi Kanu ya yi kira da kafatanin al’ummar kabilar Ibo dake Najeriya dasu kaurace ma shiga zaben 2019, a cewarsa ba zasu shiga zabe ba har sai gwamnatin Najeriya ta basu daman ballewa daga kasar.

Sai dai rundunar Yansandan Najeriya ta musanta harin, inda tace gobara ne ta kama a ofishin Yansandan dake unguwar Ajali, kamar yadda kaakakin rundunar, Haruna Mohammed ya bayyana, wanda yace tuni kwamishinan Yansandan jahar, Mustapha Dandaura ya isa ofishin.

“Iya abinda muka sani shine gobara ne ta tashi a ofishin, har sai mun samu karin bayani daga binciken sirri da muka kaddamar. Kwamishinan Yansanda, Mustapha Dandaura isa wajen don gane ma idanunsa abinda ya faru.

“Kwamishinan ya umarci mataimakin kwamishina mai kula da binciken miyagun laifuka da tattara bayanai daya gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar yadda lamarin ya wakana.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel