‘Yan Najeriya mazauna Ingila sun goyi bayan Atiku, sun bayyana dalili

‘Yan Najeriya mazauna Ingila sun goyi bayan Atiku, sun bayyana dalili

Wasu ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar Ingila (UK) sun bayyana goyon bayan su gad an takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben kujerar shugaban kasa da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

Sun bayyana cewar Atiku ne zai iya tsamo Najeriya daga kangin talauci da ci baya saboda shine zai yi shugabanci irin wanda ya dace da zamani.

Kungiyar yakin neman zaben Atiku a kasar Ingila ce ta bayyana hakan a jiya a birnin London.

Mambobin kungiyar yanzu haka sun iso Najeriya domin nema wa Atiku goyon bayan ma su kada kuri’a a zaben ranar Asabar.

A wani jawabi da su ka fitar a Abuja bayan isowar su Najeriya, sun ce babu hadi tsakanin Atiku da shugaba Buhari, mutumin da su ka ce ya gaza yin wani katabus ta fuskar inganta tattalin arzikin Najeriya.

‘Yan Najeriya mazauna Ingila sun goyi bayan Atiku, sun bayyana dalili

Atiku da Bukola a kasar Amurka
Source: Twitter

A jawabin da Dakta Tony Chidi, shugaban kungiyar ya fitar, ya bukaci ‘yan Najeriya su zabi Atiku ranar Asabar domin ya fi Buhari sanin makamar mulki.

Sai dai a daidai lokacin da wadannan mazauna kasar Ingila ke bayyana goyon bayan su ga Atiku, shi kuwa jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewar a ranar Asabar mai zuwa ne za su yi wa Atiku ritaya domin hakan ne ma fi alheri ga Najeriya.

Ban taba boye abotar da ke tsakanin da Atiku ba. Abokina ne, kuma za mu cigaba da abota bayan mun yi ma sa ritay a ranar Asabar, 16 ga watan Fabarairu.

DUBA WANNAN: Dan takarar mataimakin shugaban kasa ya goyi bayan Buhari, ya hakura da takara

“Ranar Asabar za mu yi ma sa ritaya saboda hakan ne ma fi alheri ga Najeriya da shi kan sa Atiku.

“Watakila ma har Obi za mu yi wa ritaya tare da maigidan sa domin su koma gefe su koyi tausayin talaka,” a cewar Tinubu.

Tinubu ya bayyana cewar babu wani abun kirki da Najeriya za ta ci moriya a manufofin yakin neman zaben Atiku

Tinubu ya yi wadanan kalamai ne a cikin wani jawabi da mai yada labaran sa, Tunde Rahman, ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel