Shugaban ASUU da aka dakatar ya fara manyan tone-tone

Shugaban ASUU da aka dakatar ya fara manyan tone-tone

- ASUU ta tafka yajin aiki na tsawon watanni uku

- Sun janye yajin aikin sunce a dawo, amma dalibai sunki

- Sai bayan zabe ake sa rai za'a fara karatu

Shugaban ASUU da aka dakatar ya fara manyan tone-tone

Shugaban ASUU da aka dakatar ya fara manyan tone-tone
Source: UGC

Tsohon shugaban kungiyar ASUU na bangaren jami'ar Ambrose Ali ta jihar Edo farfesa Monday Igbafen ya fara tona asiri akan dalilin da ya janyo aka dakatar dashi a yunkurin sa na maida martani.

Ya fara bayani ga manema labarai a jiya alhamis . an dai dakatar da shi ne bisa zargin cin zarafi ga mata amma ya musanta zargin inda yace da hadin bakin shugaban jami'ar akayi kutungwilar da tasa aka dakatar dashi.

Yace an dakatar dashi ne saboda ya fara bincike akan makudan kudi da hukumar tetfund ta bawa jami'ar har kasan naira biliyan biyar da rabi. Ya kara da cewa kuma bayan haka shugaban jami'ar ya bawa matarsa matsayin malamar jami'ar a babban matsayi alhalin bata cancanta ba domin kuwa bata da digiri na biyu da na uku.

GA WANNAN: Har a kotu, Atiku Abubakar ya kasa yi wa jama'a bayani kan zarginsana suwaye daga dangin Buhari masu 9-mobile

Yace ganin ya fara bincikar shi saboda wannan abun shine ya rinka bin duk hanyoyo dan ganin an dakatar dashi. Ya kara da cewa a matsayin sa na shugaban hukumar asuu yana da damar da zai binciki wannan lamarin.

Sai dai mai magana da yawun jami'ar, Mr Edward Alhevba yace ba fa iya zargin cin zarafin ne yasa aka dakatar da Prof. Igbafen ba harda wadansu manyan laifukan da ya dade yana aikatawa ana daga mishi kafa. Yace an dai fi sanin laifin ne saboda dangin wadda aka ci wa zarafin sun kai kara domin neman adalci.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel