Kiran karshe da gwamna Rochas keyi wa kabilarsa ta Igbo: In baku zabi Buhari ba, sai 2031 zaku ga Aso Rock

Kiran karshe da gwamna Rochas keyi wa kabilarsa ta Igbo: In baku zabi Buhari ba, sai 2031 zaku ga Aso Rock

- Okorocha yayi kira ga yan kabilar Igbo dasu zabi Buhari

- Yace idan suka zabi Buhari yayi nasara to suna da damar tsayar da dan takara dan kabilar Igbo a shekara ta 2023

-Wasu daga cikin yan kabilar basa goyan bayan sa suna cewa shi din makiyayi ne

Zabe: Bai kamata a bari APC

Zabe: Bai kamata a bari APC
Source: UGC

Gwamna Rochas Okorocha yace babu wanda ya kamata yan kabilar Igbo su zaba sama da Buhari a ranar Asabar idan har suna bukatar tsaida dan takarar su a shekara ta 2023.

Yace idan har suka zabi wanin hakan to saidai su jira har zuwa 2031 kafin su samu damar tsayar da Dan takarar su.

Gwamnan yayi wannan furuci ne a lokacin da yake yiwa Buhari kamfe a yankin Okigwe da Owerri a ranar Alhamis da kuma nuna nadama bisa ga abinda wasu yan siyasar Igbo sukayi na rashin goyan baya a shekara ta 2015.

GA WANNAN: Bincike: Yawan 'yan Najeriya dake cikin matsanancin Talauci ya kai 91m

Gwamnan yace "a ranar Asabar idan Igbo suka kadawa Buhari kuri'a kuma yayi nasara to suna da damar tsayar da dan takara dan Igbo a shekara ta 2023".

"Duk wani masoyin Igbo ya zama tilas ya kadawa Buhari kuri'ar sa,idan kuma muka kuskere wannan dama to bamu da wani lokacin tsayar da dan takarar mu daganan har zuwa shekara ta 2031."

Ya kara da cewa "wasu daga cikin yan uwanmu basa goyan bayan Buhari suna cewa shi din makiyayi ne dadai suransu".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel