Kunga dattijon da ya tare tun jiya a layin zabe don ya dangwalawa Buhari

Kunga dattijon da ya tare tun jiya a layin zabe don ya dangwalawa Buhari

-Wani masoyin Buhari yayi kaura daga gidansa zuwa inda zai kada kuri'a tun a ranar Laraba

- Shettima yace yana so ya kasance mutum na farko da zai kadawa Buhari kuri'a

- Yace badan Buhari ba dahar yanzu yana can a garkame

Kunga dattijon da ya tare tun jiya a layin zabe don ya dangwalawa Buhari

Kunga dattijon da ya tare tun jiya a layin zabe don ya dangwalawa Buhari
Source: Facebook

Abubakar Shettima mazaunin Duala dake Dogon Dutse karamar hukumar Jos ta arewa jihar Plateau ya koma inda zai kada kuri'ar sa a Dogon Agogo inda ya fara shirin hawa layin zaben da za'ayi a ranar Asabar.

Shettima dan shekara 59 yace yanaso ya kasance mutum na farko da zai kadawa Buhari kuri'ar sa a matsayin biyan bashin abinda yayi masa.

Shettima yabar gidansa tun a ranar Laraba sannan ya kara da cewa a shirye yake daya kara wasu awanni 48 din kafin ya kada kuri'ar tashi.

"Na riga na tura matata jihar ta ta Borno dan itama ta samu damar kada tata kuri'ar".

A halin yanzu Shettima yana zaune a wajen da ake kada kuri'ar inda ya shimfida tabarma sannan yana kire da alkurani a hannun sa yayin da katin zaben sa yake cikin aljihun sa.

GA WANNAN: Yadda ake sace namun dajin Najeriya a sayar da makudan daloli a kasashen ketare

Shettima ya bayyana yanda aka kamashi a jihar Borno sannan ake tuhumar sa da cewa shi din dan boko haram ne a shekara ta 2015.

A lokacin da Buhari ya hau mulki ya ziyarci inda ake tsare damu ya bada umarnin a ragemu a wajen saboda munyi yawa.

Sannan daga baya ya sanya aka gudanar da bincike inda aka gano cewa bamu da laifi aka sakemu.

Kafin mu tafi gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya gayyace mu inda ya bamu hakuri sannan ya mikawa kowannen mu N100,000 dan ya komawa iyalinshi.

Ya kara da cewa" bada Buhari ba da har yanzu ina can a garkame saboda haka a koda yaushe nakeyi masa addu'a kuma insha Allah zai samu nasarar zarcewa".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel