Babu maka wa sai mun samar wa Buhari kuri’u miliyan 19 – ‘One 2 Tell 10’

Babu maka wa sai mun samar wa Buhari kuri’u miliyan 19 – ‘One 2 Tell 10’

Shugaban kungiyar “One 2 To 10” mai yiwa shugaba Buhari yakin neman zabe reshen jihar Katsina, Dakta Mannir El-Yakubu, y ace babu gudu, babu ja-da-baya a kan kudirin kungiyar na samar wa da shugaba Buhari kuri’u miliyan 19 a zaben shugaban kasa na ranar Asabar.

Da yake Magana a wurin taron yakin neman zaben shugaba Buhari a jihar Katsina, El-Yakubu, y ace kungiyar su za ta tabbatar da cewar shugaba Buhari ya samu kuri’a miliyan daya daga kowacce jiha daga jihohi 19 da ke fadin arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa dandazon jama’ar da su ka halarci taron kamfen din Buhari a jihar Katsina shaida ce da ke nuna cewar mutanen jihar na tare dan su tare da bayyana cewar shugaban kasa Buhari na da daraja a duk in da ya shiga a duniya.

Kazalika, ya bayyana cewar shugaban kungiyar sun a kasa, Dakta Baffa Bichi, bait aba nuna gajiya wa ba a rangadin da kungiyar ta yi na dukkan mazabun da ke jihohin arewa 19 domin nema wa Buhari jama’a.

Babu maka wa sai mun samar wa Buhari kuri’u miliyan 19 – ‘One 2 Tell 10’

Buhari a Katsina
Source: Facebook

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar GDPN, Alhaji Ibrahim Modibbo, ya yi watsi da takarar sa tare da bayyana goyon bayan sa ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ja’iyyar APC.

DUBA WANNAN: Zabe: PDP ta bayyana matakai 4 da za ta dauka don magance magudi

Da ya ke bayyana goyon bayan na sa ga shugaba Buhari ranar Talata a Abuja, Modibbo ya ce kwazon shugaban da jam’iyyar sa a cikin shekaru uku ne babban dalilin da ya sa shi ya yanke wannan shawara.

Modibbo ya ce shugaba Buhari na da kyakyawar manufa ga Najerya da mutanen ta tare da yin kira ga jama’a da su fito kwai da kwarkwata ranar Asabar domin zazzaga wa Buhari kuri’un da za su bashi damar zarce wa a kan karagar mulkin Najeriya a karo na biyu.

Dan takarar ya kara da cewa a baya Najeriya ta sha wahala a hannun ‘yan tsirarun mutane marasa kishi da ba sa kaunar cigaban talaka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel