Buhari ya bawa 'yan Najeriya da bakin haure tabbacin yin zabe cikin lumana

Buhari ya bawa 'yan Najeriya da bakin haure tabbacin yin zabe cikin lumana

Kasa da sa’o’i 48 kafin gudanar da zaben shugaban kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranan Alhamis, 14 ga watan Fabrairu ya tabbatarwa yan Najeriya da baki daga kasashen waje samun kariya da tsaro.

Shugaban kasar ya dage kan cewa lallai za a guadanar da zabe cikin lumana, adalci da aminci.

Yayi magana na tsawon mintoci 20 a lokacinda yake gabatar da jawabi ga al’umman kasa.

Yace “a ranar Litinin, 16 ga watan Febrairu, 2019, za ayi kira gare ku don zabar shuwagabanni da zasu kaddamar da ayyika a kasarmu mai girma na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Buhari ya bawa 'yan Najeriya da bakin haure tabbacin yin zabe cikin lumana

Buhari ya bawa 'yan Najeriya da bakin haure tabbacin yin zabe cikin lumana
Source: UGC

“Wannan ya kasance yancinku na kundin tsari wanda ya cancanta wadanda suka kai shekarun kada kuri’u su fita su kada kuri’unsu.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta sake gurfanar da dan takaran gwamna na PDP a Niger da tsohon gwamna kan zambar N4.56b

“ina son in fara baiwa yan Najeriya tabbacin cewa wannan gwamnatin zata yi gwargwadon kokarinta wajen tabbatar da cewa zabukan 2019 sun gudana cikin kwanciyar hankali.

“Kuma kasancewana shugaba kuma dan kasa, ina bukatarku da ku fito ku bi sahu ku sauke hakki da ya ratawa a wuyanku da na jikokinmu da zasu zo nan gaba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel