Da dumin sa: An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa

Da dumin sa: An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa

Rahotanni daga jihar Kano dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya na nuni ne da cewa jami'an 'yan sanda sun kama wasu takardun kada kuri'a na gwaji da ke kama da ta gaskiya ta hukumar INEC da aka nufi yin amfani da su a jihar Jigawa.

Labarin batun dai yana cigaba da janyo takaddama tsakanin mabiyan jam'iyyun PDP da na APC kan abinda ake shirin yi da takardun tun bayan da ya fallasa a kafafen sadarwar zamani.

Da dumin sa: An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa

Da dumin sa: An kama samfurin takardun zabe buhu 7 a Jigawa
Source: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai iya faduwa zaben 2019 - Wani jigon APC

Legit.ng Hausa ta samu cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Kano mohammad Wakili shi ne ya bayyanawa wakilin majiyar mu hakan a ofishin sa.

Ita dai PDP tana zargin cewa APC ce ta buga takardun a wani mataki na yunkurin magudi. Shugaban kwamitin matasa na yakin neman zaben dantakarar gwamna na jam'iyyar PDP a Jigawa, Umar Danjani ne ya shaida wa majiyar mu ta BBC hakan.

Sai dai jam'iyyar APC ta musanta zargin cewa matakin wani yunkuri ne na magudin zabe, kamar yadda kakakin jam'iyyar Nasir Dahiru Jahun ya bayyana cewa samfurin kuri'un ne suka buga don wayar da kan masu zabe kamar yadda ita ma hukumar zabe ta aminta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel