APC ba ta san yadda ake magudin zabe ba – Suleiman Abba

APC ba ta san yadda ake magudin zabe ba – Suleiman Abba

- Tsohon shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya, Alhaji Suleiman Abba, ya bayyana cewa, har yanzu APCba ta san yadda a ke tafka magudin zabe ba ballatana ta aikata shi

- Abba yace murdiyar zabe wani salo ne wanda jam’iyyar PDP ta kawo a Najeriya

- Ya soki lamirin PDP da yada karairayi da farfaganda maimakon mayar da hankali wajen tallata jam’iyyar ga ’yan kasa

Tsohon shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya, Alhaji Suleiman Abba, ya bayyana cewa, har yanzu jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) ba ta san yadda a ke tafka magudin zabe ba ballatana ta aikata shi, domin a cewarsa murdiyar zabe wani salo ne wanda jam’iyyar PDP ta kawo a Najeriya.

Abba ya bayyana hakan ne a yayin gangamin da wasu mata su ka shirya a filin taro na Eagle Square da ke Abuja, don mara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben da ke tafe na ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu mai taken ‘Walk for Buhari’.

APC ba ta san yadda ake magudin zabe ba – Suleiman Abba

APC ba ta san yadda ake magudin zabe ba – Suleiman Abba
Source: Twitter

Sai ya soki lamirin PDP da yada karairayi da farfaganda maimakon mayar da hankali wajen tallata jam’iyyar ga ’yan kasa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi

Abba ya tunatar da cewa, a 2007 PDP ta sanar da lashe zabenta tun gabanin hukumar zabe wacce ke da alhakin hakan, ta ayyana sakamakon.

A cikin wadanda su ka halarci taron akwai matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jadadda jajircewar gwamnatinsa wajen magance matsalolin ta’addanci da rashin tsaro da ke addaban kasar.

Buhari wanda ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga dandazon jama’ar da suka halarci gangamin kamfen dinsa a ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu a jihar Katsina yayi alkawarin shafe ta’addanci daga kasar.

Shugaban kasar ya dauki alkawarin cewa idan har aka sake zabarsa a karo na biyu, zai yi duk iya bakin kokarinsa wajen ganin ya fitar da mutanen yankin arewa maso gabas baki daya daga kankin Boko Haram

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel