Za a samu matsala idan aka yi kuskuren sake zabar Buhari – Inji wani jigon PDP a arewa

Za a samu matsala idan aka yi kuskuren sake zabar Buhari – Inji wani jigon PDP a arewa

Jagoran yakin neman zaben dan takarar shugaban qasa a inuwar jamiyyar PDP na yankin Funtuwa Alh. Salisu Ibrahim Munafata ya bayyana cewar, idan yan Najeriya suka sake yin kuskuren zabar Shugaban kasa Muhammad Buhari uqubar yunwa, talauci da kuma rashin tsaro da suka addabi kasar nan, musamman na yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas da kuma satar jama’a sai sun fi na baya.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, Munafata ya ce, “ba fata muke yi ba, amma a irin wannan riqon sakainar Kashin da gwamnatin Buhari ke yi mana, idan mutane suka sake kuskuren da suka yi na baiwa gwamnatin Buhari dama ta shekaru hudu, sai dai muce Inna lillahi Wa’inna Ilaihirraji’una, muna fatan Allah ya canza mana da Atiku Abubakar a 2019.”

Za a samu matsala idan aka yi kuskuren sake zabar Buhari – Inji wani jigon PDP a arewa

Za a samu matsala idan aka yi kuskuren sake zabar Buhari – Inji wani jigon PDP a arewa
Source: Facebook

Ya kara da cewa “abin kunya ne a ce, Buhari ya kasa kawo karshen rashin tsaron da ya addabi al’umman kasar, musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar, babbu shakka sojoji suna iya bakin kokarin su amma gudunmawar da ya kamata gwamnatin Buhari ta basu ba ta yi kuma hakan ya nuna a zahiri gwamnatin Buhari ta gaza, siyasa kawai take yi da yaqin na yan ta’adda na cewar an rage kaifin yan qunguyar a yankin na Arewa maso gabas”.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku ya bukaci mutanen Adamawa da su zabe shi

“Wasu yan Najeriya sun saki Allah suna kallon Buhari ya yi masu aikin da Allah zaiyi, sai Allah ya zare hannun sa ya barsu da Buhari, masali yau lamarin sace mutane ya addabi yankin Arewa maso Yamma har da jihar sa Katsina, lala cewar tsaro a wannan lokacin yafi a baya, kada mu yaudari kanmu, lokaci ya yi da yan Niajeriya zazu zabi Atiku duk da cewar shi ba soja bane, amma ya qware wajen janyo qwararrun masana da suka san harkar tsaro.”

A fannin tattalin arzikjn qasa, Munafata ya ce, “Atiku ya yi fice ba wai a Najeriya kawai ba har da fadin duniya domin dan kasuwa ne shahararre ya san yadda zai farfado da tattalin arzikin kasar dake gab da durkushewa a karkashin gwamnatin Buhari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel